’Yan Boko Haram sun yi wa cibiyoyin soja barna a hare-haren Maiduguri
•Sun kone jiragen sama biyar•Sun kai farmaki ga barikin sojan sama da na kasa da Hedkwatar Shiyya ta ’yan sanda Yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kaddamar da miyagun hare-hare a garin Maiduguri hedkwatar Jihar Borno inda suka yi mummunar barna a sansanin sojojin sama wurin da suka lalata helikwaftoci biyu […]

•Sun kone jiragen sama biyar
•Sun kai farmaki ga barikin sojan sama da na kasa da Hedkwatar Shiyya ta ’yan sanda
Yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kaddamar da miyagun hare-hare a garin Maiduguri hedkwatar Jihar Borno inda suka yi mummunar barna a sansanin sojojin sama wurin da suka lalata helikwaftoci biyu da kuma jiragen sojoji uku.
Maharan sun kuma kai farmaki ga wani barikin sojojin kasa da ofishin yanki na ’yan sanda a hari mafi muni cikin wata biyar da suka gabata.
Sanarwar da kakakin rundunar sojan Najeriya, Birgediya Janar Chris Olukolade ya fitar, ta ce ’yan Boko Haram din sun kai harin ne cikin dare zuwa wayewar garin ranar Litinin, sai dai ya ce jami’an tsaro sun yi kokarin dakile harin.
A cewarsa, an kashe ’yan Boko Haram 24 a ba-ta-kashin da suka yi, a yayin da sojoji biyu suka samu raunuka.
Sai dai wasu majiyoyi na mazauna yankkin sun ce, an yi gumurzu sosai, kuma bisa dukkan alamu an samu asarar rayuka da dama a lokacin artabun.
Mazauna birnin na Maiduguri sun ba da rahoton jin karar harbe-harbe da fashewar bama-bamai a cikin birnin tun misalin karfe 1:00 na dare a ranar Lahadi.
Aminiya ta samu labarin cewa ’yan bindigar sun fara kai hari ne ga rajimantin atilare na 33 na sojojin Najeriya da ke hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, inda suka ruguza mafi yawan gine-ginen da ke wurin. Wasu da suka ga abin da ya faru sun ce an kona kusan baki dayan gine-ginen da ke barikin, kuma ana fargabar cewa harin ya ritsa da mutane da dama.
Daga nan maharan suka gusa zuwa bangaren sojan sama inda suka ruguza mafi yawan kayayyakin da ke wurin da suka hada da helikwaftoci da motoci da wuraren gyaran motoci da ofisoshi da kuma gidajen jami’ansu. Bincike ya tabbatar da cewa harin ya fi muni a wurare biyu da suka hada da sansanin sojojin saman Najeriya da ke makwabtaka da filin saukar jiragen sama na Maiduguri da kuma barikin sojojin kasa da ke wajen birnin na Maiduguri. Kuma daga nan ne maharan suka dumfari Hedkwatar Shiyya ta ’Yan sanda da ke Bulunkutu inda suka lalata daukacin ginin.
Sama da motoci 100 da suka hada da na jami’an tsaro da na mayakan Boko Haram da kuma na fararen hula aka kona. Yayin da gidajen mai da wasu gidajen jama’a da ke kusa su ma suka sha wuta.
Wakilin Aminiya da ke tare da wasu jami’an gwamnati ya ruwaito cewa ya ga wasu motoci kirar Hilud dauke da bindigogin harbor jiragen sama a yashe da ake zargin ’yan Boko Haram sun gudu sun bari.
Majiyar jami’an tsaro ta ce sun ci karensu babu babbaka a tsawon lokacin da suka gudanar da wadannan hare-hare musamman tsakanin karfe 3:30 zuwa karfe 8:00 na safe.
Wani mazaunin Rukuninn Gidaje na 777 da ke kusa da matsugunin sojojin saman mai suna Salisu Baba ya ce harin “Kamar tashin duniya ne. A rukunin gidajenmu bangaren da ’yan sanda suke an ruguza shi, kuma an bindige mutum biyu da ke tsare.”
Baba ya ce maharan suna da dimbin yawa, “sama da mutum 2000, wasu dauke da bama-bamai, wasu da bindigogin harbor jiragen sama, wasu kuma dauke da bindigogi kirar AK 47. Na hango su ta tagar gidana, kuma matata ma ta gansu,” inji shi.
Wani jami’in tsaro ya ce sai dai jirgin yaki ya zo daga Yola ta Jihar Adamawa sannan maharan suka ja da baya.
Gwamnatin Jihar Borno a nata bangaren ta kafa dokar hana fita ta sa’o’i ashirin da hudu a kwaryar birnin na Maiduguri, lamarin da ya tilasta wa matafiya da dama da ke kan hanyarsu ta zuwa birnin komawa inda suka fito sakamakon dokar da aka kafa.
A bangaren guda kuma, hukumar kula da filayen saukan jiragen sama ta Najeriya ta tabbatar da cewa harin bai shafi filin saukan jiragen saman Maiduguri ba, amma duk da haka ta rufe filin zuwa wani lokaci saboda dalilai na tsaro.
Shugaba Goodluck Jonathan ya gana da hafsoshin tsaron kasar sakamakon wannan harin, sai dai babu dai wani bayani a kan abin da suka tattauna, amma hafsoshin tsaron sun tabbatar da cewa an shawo kan lamarin.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki kadan bayan da rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kai hare-hare a dajin Sambisa, inda ta ce ’yan Boko Haram na da sansani.
An maido da layukan wayoyin salula a Maiduguri
Rahotanni daga Jihar Borno sun cewa an maido da layukan wayar salula a birnin Maiduguri da kewaye.
Jihar dai na daya daga cikin jihohi uku da aka sanya wa dokar ta-baci a watan Mayun da ya gabata saboda tabarbarewar tsaro, lamarin da ya sanya aka katse ta daga hanyoyin sadarwa na wayoyin salula.
An maido da wayoyin sadarwa a jihohin Adamawa da Yobe da ke makwabtaka da Jihar Borno, inda aka ci gaba da hana hanyar sadarwar a jihar.
A halin yanzu mutane na iya kiran ’yan uwansu da ke jihar bayan shafe watanni ba tare da sada zumunci ba.
Matakin dawo da wayoyin sadarwar na zuwa ne kwana daya bayan da ’yan Boko Haram suka kai munanan hare-hare a cibiyoyin jami’an tsaro da ke Maiduguri.
Shugaba Goodluck Jonathan ne ya kafa dokar ta-baci a jihohin Adamawa da Yobe da kuma Borno don murkushe ayyukan ’yan kungiyar Boko Haram, sai dai jama’ar jihohin sun rika kukan cewa katse sadarwar ba ta magance komai game da hare-haren da ake kai wa jihohin ba.