’Yan Burkina Faso sun yi gangamin kin jinin karin wa’adi ga shugaban kasa
dimbin ’yan Burkina Faso sun halarci wani gangami da aka shirya a filin wasa da ke babban birnin kasar, Ouagadougou, a wani mataki na bayyana adawa da kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Shugaban kasar Blaise Campaore zai gabatar don neman karin wa’adin mulki.Gangamin da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata ya samu halartar mutum […]

dimbin ’yan Burkina Faso sun halarci wani gangami da aka shirya a filin wasa da ke babban birnin kasar, Ouagadougou, a wani mataki na bayyana adawa da kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Shugaban kasar Blaise Campaore zai gabatar don neman karin wa’adin mulki.
Gangamin da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata ya samu halartar mutum fiye da dubu 45, kuma ya zo ne wata guda bayan magoya bayan shugaban kasar sun gudanar da wani gangami da ke maraba da gudanar da kuri’ar.
Jagoran ’yan adawar kasar, Zephirin Diabre ya fadawa taron cewa “ba ma bukatar kara tsawon wa’adin shugabancin kasa nan saboda mulkin Burkina Faso ba mulki ba ne irin na mutu ka raba. Jamhuriya ce da shugabanni ke zuwa kuma in lokacinsu ya yi, su tafi”.
Shugaba Compaore ya dare kan karagar mulki ne bayan wani juyin mulki da ya jagoranta a shekarar 1987. Ya na samun goyon bayan kasashen Yamma ne saboda yadda yake taimakawa wajen yaki da mayakan da ake dangantawa da kungiyar al-kaeda a yankin Yammacin Afrika.
Bai kai ga bayyana bukatarsa ba, amma akwai alamun da ke nuni da cewa ya na da aniyar canza kundin tsarin mulkin kasar don ya samu damar ci gaba da mulkinsa.
Har ila yau, ’yan adawar kasar sun ce za su jagoranci wani gagarumin gangami a ranar 14 ga watan nan, a gari na biyu mafi girma a kasar, wato Bobo Dioulasso, wanda daga shi ne kuma suke fatan ya rikide zuwa zanga-zangar game gari.