’Yan canji dubu 2 da 442 ne suka cika sharuddan babban Bankin Najeriya

A makon da ya wuce, Babban Bankin Najeriya ya fitar da jerin sunayen kamfanonin cbanjin kudi da suka cika ka’idojin samun lasisin hada-hadar canji, wadanda yawansu ya kai dubu biyu da 442, wato bisa sabon tsarin tanadar wani adadin a matsayin sharadin gudanar da harkokin kasuwancinsu.Don haka aka soke lasisin Kamfanonin canjin kudi har 766, […]

’Yan canji dubu 2 da 442 ne suka cika sharuddan babban Bankin Najeriya
’Yan canji dubu 2 da 442 ne suka cika sharuddan babban Bankin Najeriya

A makon da ya wuce, Babban Bankin Najeriya ya fitar da jerin sunayen kamfanonin cbanjin kudi da suka cika ka’idojin samun lasisin hada-hadar canji, wadanda yawansu ya kai dubu biyu da 442, wato bisa sabon tsarin tanadar wani adadin a matsayin sharadin gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Don haka aka soke lasisin Kamfanonin canjin kudi har 766, tyare da wasu dubu da 500, wadanda ke gudanar da hada-hada bisa ka’ida, amma sun kasa cika sharaddan sabon tsari.
Tun a watan Yunin bana, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake tsarin hada-hadar canjin kudi, inda ya kara yawan kudin garkuwar asara da kamfanonin canji za su ajiye na Naira miliyan 35, matukar suna son gudanar da hada-hadar kasuwancinsu a kasar nan, sabanin yadda a da Naira miliyan 10 ne.
Don ganin cewa, ’yan canjin sun samu damar cika sharuddan da aka gindaya musu, sai babban bankin ya kara wa’adin kwanakin zuwa 31 ga watan Yulin da ya gabata, sabanin 15 ga wata da aka sanya a da.
Kafin a fito da wannan sabon tsarin akwai ’yan canji masu rajista har dubu uku da 208, da kuma wasu dubu da 500 da suka samu amincewar fara hada-hada.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele. Ya bayyana cewa, an fito da sabon tsarin ne, ganin yadda kamfanonin ’yan canji suka kauce daga kan manufar da ta sanya aka ba su lasisi.
A cewarsa, Babban Bankin ya gano cewa mafi yawancin masu ahda-hadar, su samu dimbin riba daga canjin kudaden kasashen waje, ba tare da la’akari da tanadin doka ko tsarin canjin kudi da ake amfani da shi a banki.