’Yan canji sun kalubalanci matakin Babban Bankin Najeriya

Gamammiyar kungiyar masu canjin kudaden kasashen waje a karkashin cibiyar canji ta Al’Amanat ta bayyana rashin gamsuwarta da dokar Babban Bankin Najeriya da ya a bukaci kowane mai canji sai ya ajiye Naira miliyan 35 a asusun ajiyarsa na bankin kafin a kyale shi ya ci gaba da harkarsa ta canji.A yayin da yake zantawa […]

’Yan canji sun kalubalanci matakin Babban Bankin Najeriya
’Yan canji sun kalubalanci matakin Babban Bankin Najeriya

Gamammiyar kungiyar masu canjin kudaden kasashen waje a karkashin cibiyar canji ta Al’Amanat ta bayyana rashin gamsuwarta da dokar Babban Bankin Najeriya da ya a bukaci kowane mai canji sai ya ajiye Naira miliyan 35 a asusun ajiyarsa na bankin kafin a kyale shi ya ci gaba da harkarsa ta canji.
A yayin da yake zantawa da Aminiya a kan al’amarin, Mataimakin Shugaban kungiyar, Alhaji Abdulhamid Kabir ya bayyana cewa kudin ajiyar da Babban Bankin ya saka musu ya yi yawa kwarai da gaske, musamman ma duba da halin kuncin rayuwa da karancin kudin da ake fama da shi a yanzu.
Haka nan ya bayyana cewa wa’adin da Babban Bankin ya saka musu na zuwa karshen wannan watan, wato nan da kasa da mako daya, ya yi kadan kwarai da gaske. Ya ce, “idan aka duba lokacin mulkin siyasa muke ciki na Dimokuradiyya ba wai mulkin soja ba, kuma mu ne muka jefa kuri’a muka zabi wannan gwamnatin, don haka bai kamata ta kawo tsarin da zai takura wa jama’a ba.”
Ya kara da cewa sabuwar ka’idar da abban bankin ya fito da ita ta tayar da hankulan masu canjin kudaden matuka da gaske, inda wadansu da dama ma sun kwanata rashin lafiya a saboda hawan jini da ya same su saboda damuwar tunanin yadda za su iya samo kudin ajiyar na Naira miliyan 35 da aka sanya musu.
Ya ce a saboda haka, “muna kira ga Gwamnan Babban Banki da ya sake duba wannan doka, ya kara mana lokacin biyan kudin ajiyar sannan kuma ya rage mana yawan kudin da ake bukata mu biya na ajiyar.” Ya ce a sakamakon hakan yanzu da dama sun daga kamfanoninsu na canji za su sayar kuma ya ki sayuwa, sannan kuma ya ce idan har ba a sauya dokar ba, mutane da dama za su rasa aikin yi domin ba su san wata sana’a ba idan ban da ta canji.