’Yan canji sun koka kan sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya ya fitar game da harkokinsu

kungiyar ’Yan Tireda da Canjin Kudi ta Abuja ta koka kan sabon tsarin da Babban BankinNajeriya ya fitar game da harkokinsu.Shugaban kungiyar Alhaji Salihu Umar Garu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya a Abuja shekaranjiya Laraba.A ranar Litinin ne Babban Bankin Najeriya ya fitar da sanarwar mafi karancin jarin […]

’Yan canji sun koka kan sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya ya fitar game da harkokinsu
’Yan canji sun koka kan sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya ya fitar game da harkokinsu

kungiyar ’Yan Tireda da Canjin Kudi ta Abuja ta koka kan sabon tsarin da Babban BankinNajeriya ya fitar game da harkokinsu.
Shugaban kungiyar Alhaji Salihu Umar Garu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya a Abuja shekaranjiya Laraba.
A ranar Litinin ne Babban Bankin Najeriya ya fitar da sanarwar mafi karancin jarin fara canji ya tashi daga Naira miliyan 10 zuwa 35, sannan ‘kudin ajiya’ a bankin da babu ruwa ya tashi daga Naira miliyan 3 zuwa Naira miliyan 35. Kudin sayan fom yana nan kan Naira dubu 100, inda aka daga kudin mallakar lasisi daga Naira dubu 500 zuwa Naira miliyan 1, sannan kudin sabunta lasisi na shekara-shekara ya karu daga Naira dubu 10 zuwa Naira dubu 250.
Shugaban kungiyar ya ce: “Wannan sabon tsari mai karin kashi 250 da Babban Bankin Najeriya ya fitar zai shafi yadda muke gudanar da harkokinmu. A yanzu haka da yawa daga cikin kwastomominmu sun fara fargabar yadda abubuwa za su kasance a gaba.”
Ya ce babban abin takaici shi ne, Babban Bankin Najeriya bai zauna da su don ya yi musu bayanin yadda al’amarin zai kasance ba, bai kuma sanar da yawan Dalar da zai ba su ba, ya dai bayyana yawan kudin da yake so a ajiye ne kawai ne.
Ya ce hakan ba daidai ba ne, “Kodayake za a iya danganta rashin yin hakan da rikicin da ya dabaibaye kungiyarmu ta ABCON.”
“A yanzu haka muna neman mafita a kungiyance, domin Kano sun yi zama jiya (Talata), Legas da Fatakwal ma za su yi zama, mu kuma yau (shekaranjiya Laraba) muka yi zama, daga nan za mu yi babban taro don ganin yadda za mu tunkari al’amarin.”
Hashim Ibrahim wani dan canjin kudi ya ce sabon tsarin yana ba shi tsoro, domin ba kowa ba ne zai iya cika wannan ka’idar ba.
“karin kashi 250 ba kadan ba ne, sannan Babban Bankin Najeriya ya bayar da karamin lokaci, wato zuwa 15 ga watan gobe. Abin damuwar shi ne, idan lokacin ya wuce za a kwace lasisin duk wanda bai cika ka’idar ba. Hakan zai kawo mana cikas.” Inji Hashim.
Ahmad Idris wanda ya canja Dala zuwa Naira ya ce, tun da ya karanta labarin sabon tsarin ya shiga damuwa, domin a tunaninsa hakan ba zai haifar da da mai ido ga harkar canji ba.
Bashir Isah wanda shi ma ya canja Naira zuwa Riyal ya ce, ba ya tsammanin sabon tsarin zai kawo wa harkar canji cikas.