’Yan China na yunkunrin kassara mana sana’a — ’Yan Gwangwan
An kyale bakin haure suna neman kwace wa ’yan kasa sana’a.
Sarkin ’Yan Gwangwan na jihohin Yamma, Alhaji Ibrahim Abdullahi Soja ya bayyana cewa mutanen China sun shigo kasuwar gwangwan a Najeriya, inda suke neman kassara ta, su lalatata amma an zuba musu ido, an ki daukar mataki a kan lamarin.
Ya ce sana’ar gwangwan na sahun gaba a Najeriya wajen samar wa dimbin jama’a aikin yi da hanyoyin dogaro da kai, musamman matasa da ke mai da hankali kan sana’ar, duba da rashin aikin yi.
- Gwamnan Oyo ya ba masallatan Hausawa gudunmuwar motoci
- EU ta yi Allah wadai da harba makami mai linzami kan Japan
Ya kuma ce akwai tarin matasa da suka kammala karatu a fannoni da dama kuma suke dogaro da sana’ar gwangwan, sai dai abin takaicin shi ne mahukunta sun zuba ido suna kallon bakin haure daga China sun shigo kasar, suna yi wa sana’ar hawan kawara.
“Mun yi iya kokarinmu domin ganin an yi maganin abin amma hakan ya ci tura, har yajin aiki kungiyarmu ta kasa ta yi amma duk a banza.
“An kyale bakin haure suna neman kwace wa ’yan kasa sana’a.
“Yadda abin yake a baya, masana’antu ne ke sayen kaya a wajenmu, za mu bai wa yara kudi su je su nemo kaya su saya su kawo mu ba su ribarsu, mu kuma mu kai kamfani su saya a hannunmu.
“Amma yanzu an wayi gari dan China zai hauro yana shiga loko da sako yana sayen kaya a hannun yara, yana kai wa kamfani, ya gyara ya tafi da su kasarsu.
“An kuma zuba ido ana gani, a haka ne ake so kasarmu ta samu ci gaba?” inji shi.
Sarkin ya kara da cewa a matsayinsu na shugabannin kasuwar gwangwan a Yammacin Najeriya, suna iya kokarinsu domin tsaftace sana’ar, domin akwai bara-gurbin da ke neman bata wa sana’ar suna a ko wane lokaci.
Ya ce kuma mafi akasarin masu bata wa sana’ar suna ba ’yan gwangwan ba ne, barayi ne kawai.
A cewarsa, “shi dan gwangwan ba ya daukar kayan jama’a ko kayan gwamnati, sai dai ya sayi kayan da ba a so, wanda muke kira sikirab amma duk wanda ka ga ya dauki kayan jama’a ko ya sayi kayan sata, to ba dan gwangwan ba ne, barawo ne” inji shi.