‘Yan daba ne suka haddasa rikici a Kasuwar Sasa – ‘Yan sanda

Tun ranar Asabar da ta gabata ce ’yan kasuwa Yarbawa da Hausawa da ke hada-hadar kasuwanci a Kasuwar Sasa a Ibadan, suka ci gaba da harkokinsu bayan barkewar rikicin da ya auku cikin dare ranar Alhamis din makon jiya. Rikicin ya haifar da girke jami’an tsaro da mahukunta suka yi don hanzarta kwantar da lamarin. […]

‘Yan daba ne suka haddasa rikici a Kasuwar Sasa – ‘Yan sanda

Tun ranar Asabar da ta gabata ce ’yan kasuwa Yarbawa da Hausawa da ke hada-hadar kasuwanci a Kasuwar Sasa a Ibadan, suka ci gaba da harkokinsu bayan barkewar rikicin da ya auku cikin dare ranar Alhamis din makon jiya. Rikicin ya haifar da girke jami’an tsaro da mahukunta suka yi don hanzarta kwantar da lamarin. Mahukuntan sun tabbatar da cewa, wadansu ’yan daba ne daga wajen kasuwar suka haddasa rikicin ta hanyar shiga cikin kasuwar da suka rika farfasa shaguna da raunata mutane da satar kudade da kayan abinci.

Da sanyin safiyar ranar Juma’a da ta wuce ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu ya jagoranci manyan jami’ansa domin ziyarar gani da ido a kasuwar ta Sasa. Bayan kammala ziyarar ce Kwamishinan ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa rikici ne a tsakanin ’yan kasuwa Yarbawa da Hausawa inda ya ce babu kanshin gaskiya a wannan rahoto.

Ya ce, bincike ya nuna cewa wadansu ’yan daba dauke da makamai ne suka tayar da zaune-tsaye domin satar kayan jama’a. Ya ce, mutum tara ne suka samu raunuka a yayin da aka kama mutum shida da ake zargi da haddasa rikicin. Ziyarar kasuwar da Aminiya ta yi ta gane wa idonta yadda ’yan kasuwa Yarbawa da Hausawa suka ci gaba da hada-hadar kasuwanci bayan rufe kasuwar na wunin Juma’a.

Aminiya ta zanta da Alfa Wasiu Dankashi, wanda ya ce “Shekara 30 da ke nan da muke harkokin kasuwanci da ’yan uwanmu Hausawa lami lafiya a wannan kasuwa. Wallahi wadansu ’yan iska ne suka shigo kasuwa cikin dare suka fasa shaguna amma babu fada ko rikici a tsakanin mu Yarbawa da Hausawa a wannan kasuwa.”

Hajiya Mujidatu ta tsine wa duk wanda ya haddasa rikicin. Ta ce, “Karya ne babu rikici tsakaninmu da Hausawa domin kai ma ka gani da idonka na zo na sayi kayan abinci a wurin Bahaushe a cikin kasuwa.”

Shugaban Kasuwar Sasa, Alhaji Usman Yako wanda aka lalata wani sashe na ofishinsa ya jinjina wa jami’an tsaro kan hanzarta shawo kan lamarin. Ya ce “A cikin dare ranar Alhamis na samu labarin wadansu yara da babu abin da ya shafe su da kasuwa sun shigo suna fasa shaguna da sarar jama’a. A lokacin ne na sanar da DPO da Kwamandan yanki suka sanar da Kwamishinan ’Yan sanda wanda ya hanzarta bayar da umarnin girke jami’ansa da sojoji suka shawo kan lamarin.”