’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai

Wasu ’yan daba sun gine-ginen makaranta a yankin Okpoga da ke Karamar Hukumar Okpogwu da ke Jihar.

’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai

Wasu ’yan daba sun gine-ginen makaranta a yankin Okpoga da ke Karamar Hukumar Okpogwu da ke Jihar.

Ɓata-garin sun ƙona gine-ginen ne a Makarantar Sakandaren Central UBE da ke Ogwu-Okpoga da kuma Makarantar Ƙaramar Sakandare s ake Obossa.

Wani shaida ya bayyana wa wakilinmu cewa a makon da ya gabata ne ’yan daban suka yi wannan aika-aika. Shaidan wanda bai amince a bayyana sunansa ba, ya yi zargin wata manufar siyasa ce ta sa ’yan daban suka cinna wa gine-ginen wuta. Ya bayyana damuwa kan yawaitar irin wannan aika-aika a ’yan kwanakin nan.

Kokarinmu ma ji daga kakakin ’yan sanda ta Jihar Binuwai, Catherine Aneneh, bai yi nasara ba, saboda mun kira ta a waya ba ta shiga ba.

Amma a ƙarshen mako ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar Binuwai ta Kudu kuma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moroh, ya ziyarci makarantun da abun ya shafa a ƙarshen mako.

Abba Moroh ya yi tir da lamarin tare da mamakin dalilin ƙona cibiyoyin ilimi da ake rainon manyan gobe.

Daga nan sai ya yi alƙawarin sake gina ajujuwan yana mai kira ga al’ummar yankin da su tashi domin kare ababen more rayuwar da aka samar musu.

Dan majalisar ya kuma ziyarci babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Yankin Okpoga, inda ya jinjiya musu bisa ƙoƙarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Sai dai ya koka bisa mummunan halin da ofishin yake ciki, sannan ya yi alƙawarin yi masa kwaskwarima.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya?

HOTUNA: Abba ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano

’Yan bindiga sun kashe fasto a Gombe

An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila