’Yan daba sun aika ’yan bindiga lahira a Kaduna
’Yan dabar sun kone ’yan bindigar kurmus bayan da suka yi wa wani dan kasuwa kwace
Mazauna kananan hukumomin Sanga da Lere a Jihar Kaduna sun kashe wasu ’yan bindiga a jajibirin Kirsimeti, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gidan Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce ’yan daba sun kashe wasu ’yan bindiga a jihar.
- Mutum 12 sun bakunci lahira a hanyar Kaduna zuwa Abuja, 25 sun jikkata
- El-Rufai ya sallami Sakatarorin Ilimi 23 a Jihar Kaduna
- Covid-19: Sabbin matakan kariya da Gwamna El-Rufai ya gindaya a Kaduna
- COVID-19: El-Rufai ya umarci ma’aikatan Kaduna su yi aiki daga gida
“A ranar 24 ga Disamba 2020, ’yan bindiga a Karamar Hukumar Sanga sun farmaki wani dan kasuwa suka kwace masa kudi da wasu muhimman abubuwa.
“Kafin zuwan jami’an tsaro wajen, sai suka tarar wasu ’yan daba sun kone ’yan bindigar har lahira,” inji Aruwan.
Ya kara da cewa wasu ’yan bindiga sun bude wa mutane wuta a kan hanyar Aboro-Kafanchan, inda harsashi ya samu wani mutum mai suna Richard Sabo.
Nan take Sabo ya take daya daga cikin ’yan bindigar, shi ma daga bisani rai ya yi halinsa bayan an kai shi Babban Asibitin Gwantu.
A ci gaba da ceaw a kauyen Domawa da ke Karamar Hukumar Lere, wasu ’yan bindiga uku su ma sun gamu da ajalinsu.
’Yan bindigar sun kware wajen satar dabbobi da kuma kwacen kayan mutane, amma a wannan karon mutanen kauyen sun musu kofar rago.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun fille kan wani dan acaba mai suna Hudu Yahaya mazaunin kauyen Unguwan Nungu, da ke Karamar Hukumar Sanga.
Aruwan ya ce Gwamna El-Rufa’i ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wanda suka rayukansu a hannun ’yan bindigar.
Sannan gwamnan ya ja hankalin mutanen jihar da su kauce wa daukar doka a hannunsu.