’Yan daba sun bude wa masu zabe wuta a Bayelsa

Wasu ’yan bangar siyasa sun bude wa jama’a wuta tare da sace kayan zabe a yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Bayelsa.

’Yan daba sun bude wa masu zabe wuta a Bayelsa

Wasu ’yan bangar siyasa sun bude wa jama’a wuta tare da sace kayan zabe a yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Bayelsa.

’Yan bangar siyasanan sun kai harin ne a wasu rumfunan zabe a kananan hukumomin Ija ta Kudu da kuma Sabgama, insa suka rika harbe-harbe suna tafiya da kayan zabe.

Maharan sun fatattaki masu zabe suka kwashe kayan zaben a yankin Agorogbene, rumufanan zabe masu lamba 6, 7 da 8 gunduma ta 11 da kek Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu.

Masu zabe sun nemin yin fito-na-fito da ’yan bangar siyasan, amma suka mayar da martani da harbe-harbe.

Da misalin karfe 9 na safe wasu bata-garin sun kai hari a cibiyar tattara sakamakon zabe inda suka yi awon gaba da kayan zaben biyar daga cikin mazau bakwai.