’Yan daba sun daddatsa dan sanda a Kano

Fadan dai ya barke ne tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan daba guda biyu

’Yan daba sun daddatsa dan sanda a Kano

Rikici

’Yan daba sun kashe wani jami’in dan sanda yayin wani fada tsakanin kungiyoyin ’yan daba guda biyu a unguwar Yakasai da ke birnin Kano.

Lamarin, a cewar wani ganau, ya faru ne wajen misalin karfe 6:00 na yammacin Talata, lokacin da wani dan daba da ya sauka daga babur din Adaidaita Sahu a kusa da Asibitin kwararru na Maurtala Muhammad da ke Kano, abokan fada kuma suka hau shi da sara.

Majiyar, wacce ba ta amince a bayyana sunanta ba, ta ce, bayan saukar mutumin ne daga kan babur din sai wasu ’yan dabar da ba sa ga maciji suka far masa da makamai.

“Sai da ’yan sanda suka kwashe kusan minti 10 kafin su tarwatsa su, inda ’yan dabar suka juyo kan ’yan sanda suka fara jifan su.

“Lokacin da ’yan sandan ke kokarin guduwa ne sai daya daga cikinsu ya fado daga kan mota, inda nan take ’yan dabar suka hau saran shi, ba ji ba gani. Tuni ma ya riga mu gidan gaskiya,” in ji majiyar.

Majiyar ta kara da cewa an shafe tsawon kwanaki ana fuskantar fadan daba a unguwar.

Da wakilinmu ya tambayi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har yanzu ba su samu rahoton kisan ba, amma suna nan suna bincike a kai don gano gaskiyar abin da ya faru.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta