’Yan daba sun fatattaki masu zanga-zanga a Legas
Zanga-zangar dai ta zama tashin hankali a wasu yankuna na Najeriya.
Wasu ’yan daba sun fatattaki masu zanga-zanga a yankin Alausa, inda ofishin gwamnati Jihar Legas yake.
Aminiya ta ruwaito cewa ofishin Gwamna Babajide Sanwo-Olu yana yankin Alausa, inda masu zanga-zangar suka yi cincirindo tun bayan fara zanga-zangar a faɗin kasar a ranar Alhamis.
- HOTUNA: Yadda Ake Zanga-zanga Da Tutocin Rasha A Arewa
- Yanzu-Yanzu: An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya
Masu zanga-zangar sun ki komawa filin Freedom Park da ke Ojota, wajen da kotu ta amince musu su yi zanga-zanga a Legas.
Da misalin ƙarfe 12 na rana, wasu ’yan daba suka kai musu hari da makamai.
Masu zanga-zangar sun yi ta kansu, inda kowa ya cika wandonsa da iska.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro da wajen ba su ɗauki mataki ba yayin da masu zanga-zangar suka tsere daga yankin.
Wannan lamarin ya faru ne bayan awanni 24 da ’yan daba suka hana masu zanga-zangar taruwa a filin Freedom Park da ke jihar.