’Yan daba sun hallaka matashi a Kaduna

Wasu ’yan daba da ba a san ko su wane ne ba, sun hallaka wani matashi mai shekara 22 mai suna Shamsudeen Albdulhamid a ranar Talatar da ta wuce a Unguwar Rimi, Kaduna. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ’yan dabar su akalla 20 ne suka isa unguwar a cikin Keke NAPEP inda suka […]

’Yan daba sun hallaka matashi a Kaduna
’Yan daba sun hallaka matashi a Kaduna

Wasu ’yan daba da ba a san ko su wane ne ba, sun hallaka wani matashi mai shekara 22 mai suna Shamsudeen Albdulhamid a ranar Talatar da ta wuce a Unguwar Rimi, Kaduna. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ’yan dabar su akalla 20 ne suka isa unguwar a cikin Keke NAPEP inda suka rika sarar duk matashin da suka gani a unguwar. Marigayin wanda kafinta ne ajali ya riske shi ne a kan hanyarsa ta zuwa wurin sana’arsa a kan Titin Jama’a da ke unguwar. Wani wanda abin ya faru a kan idonsa mai suna Usman ya ce ’yan dabar sun far wa marigayin ne da sara da wukake da adduna inda daga bisani suka yi amfani da dutse wajen kwankwatsa masa kai. “Lokacin da suka far wa marigayi Shamsudeen da sara da wukake da adduna sai suka rika ihu suna cewa duk wanda ya isa ya zo ya cece shi suna jiransa. Amma saboda irin makaman da ke hannunsu babu wanda ya karasa wurin domin kowa gudu yake yi, hakan ya sa suka gama abin da suke ba tare da an tukare su ba,” inji shi. Mahaifiyar marigayin Hajiya Husaina Abubakar da ke titin Shehu Laminu ta ce dan nata ya je ya gaishe ta kafin ya wuce wurin sana’arsa da misalin karfe 8.10 na safe. Ta ce bayan misalin minti 40 sai aka kira ta cewa wai danta na kwance a mace a asibitin Barau Dikko. Ta ce danta mutum ne da ba ya son fada, kuma ba ta tsammanin yana fada da wasu a unguwar. Kakakin ’Yan Sandan Jihar, DSP Zubairu Abdullahi ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce tuni an tura ’yan sanda unguwar domin maido da doka da oda.