’Yan daba sun hallaka matashi a Kano
Wani matashi mai suna Sadik Kabir Tudun Murtala ya rasa ransa sakamakon saran da ake zargin ’yan bangar siyasa sun yi masa a Kano.
Wani matashi mai suna Sadik Kabir Tudun Murtala ya rasa ransa sakamakon saran da ake zargin ’yan bangar siyasa sun yi masa a Kano.
Freedom Radio ta rawaito cewa lamarin ya faru ne lokacin da wani dan siyasa ya je yakin neman zabe Karamar Hukumar Ungoggo, inda wasu daga cikin magoya bayansa suka afka wa al‘ummar yankin.
- Canjin kudi da wahalar mai sun kai ’yan Najeriya bango
- Wadanda suka rasu a girgizar kasar Turkiyya da Syria za su kai 20,000 —Jami’an lafiya
Wani matashi mai suna Abubakar Adamu da lamarin ya ritsa da shi, ya ce mummunan saran da aka yi wa matashin ne ya yi ajalinsa.
“Mun taso daga Dantamashe zan tafi Rimin Kebe, a kan hanyarmu sai mai Keken da nake ciki ya ce zai yanke ta lunguna saboda ya ga wani dan siyasa ya zo da ’yan daba da makamai.
“Amma duk da haka sai da lamarin ya rutsa da mu, suka fasa gilas din A Daidata Sahun da muke ciki, mu kuma sai muka fita da gudu. Kowa suka samu sara suke, nan suka sari matashin,” in ji shi.
Shi ma wani dan uwan margayin mai suna Kabir Adam ya ce dan uwan nasa na wurin sana’arsa aka kashe shi.
“Wurin sana‘arsa ya je lamarin ya rutsa da shi kuma kowa ya shaida ba makami a hannunsa ko jikinsa sanda lamarin ya faru. Hasalima yaro ne mai shekaru 18 ba wani babba ba.”
Ita ma marikiyar margayin mai suna Zuwaira ta ce sam al’amarin bai yi musu dadi ba.
“Daga gida ya fita bayan ya yi wanki, sai ya min sallama ya tafi wurin sana‘arsa a gidan ruwa, dawowar da bai yi ta ba da rai kenan. Sun sare shi a ka har sai da ya mutu,”in ji ta.
A nasa bangaren kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba su da labarin afkuwar lamarin, amma dai za su bincika.