’Yan daba sun hallaka sintiri biyu a Kaduna

… dan sintiri ya kashe magidanci kan zargin satar shanu Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun far wa wasu ’yan sintiri da aka fi sani da ’yan kato da Gora a Hayin Rigasa da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna inda suka kashe biyu daga cikinsu. Rahotanni daga yankin sun ce ’yan […]

’Yan daba sun hallaka sintiri biyu a Kaduna
’Yan daba sun hallaka sintiri biyu a Kaduna

… dan sintiri ya kashe magidanci kan zargin satar shanu

Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun far wa wasu ’yan sintiri da aka fi sani da ’yan kato da Gora a Hayin Rigasa da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna inda suka kashe biyu daga cikinsu.

Rahotanni daga yankin sun ce ’yan dabar sun far wa ’yan sintirin ne a lokacin wani farmaki da aka kai da nufin cefke su a maboyarsu. Al’amarin ya faru ne a Layin ’Yan Kifi da ke a Hayin Rigasa a ranar Alhamis din makon jiya.
Aminiya ta samu bayanin cewa daya daga cikin ’yan sitirin ya rasu ne a lokacin artabu da ’yan dabar sakamakon sararsa da suka yi, yayinda dayan ya rasu bayan ya dan yi jinya sakamakon raunukan da ya samu a artabun.
daya daga cikin masu rike da sarauta a garin Hayin Rigasa da bai son a ambaci sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa: “Gaskiya wannan abu bai yi dadi ba, saboda irin ayyukan ’yan dabar nan na damunmu a wannan gari na Hayin Rigasa. Kuma mun kafa ’yan sintirin ne domin su taimaka wajen kare mutanen yankin daga ’yan dabar. Kuma ’yan sintirin matasa ne na garin Hayin Rigasa da ke da kishin ganin an gyra wannan gari, amma sai ga shi wadannan ’yan daba sun kai musu hari har sun yi sanadin mutuwar biyu daga cikinsu.”
Ya ce tunda abin ya faru a makon jiya gabata aka turo jami’an ’yan sanda na musamman inda suka yi nasarar kama mutum hudu daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin, sauran biyun kuma sun gudu su da iyayensu domin tsoron kamu. “Saboda dama mun zauna mun amince a tsakaninmu cewa duk wanda dansa ya je ya sari wani da wuka idan ’yan sanda suka zo kama shi idan ba a gan shi ba za a kama iyayensa,” inji shi.
A wani dan sintiri mai suna Abdul Halidu ya hallaka wani Bafulatani mai suna Sama’ila Adamu bisa zarginsa da satar shanu a karamar Hukumar Igabi.
Wanda aka kashen yana da mata uku da ’ya’ya bakwai kuma a cewar iyalansa dukkan matansa uku na dauke da juna biyu.
dan uwan Sama’ila mai suna Jafar Y. Mugero ya shaida wa Aminiya cewa:“dan uwana Sama’ila Adamu ya tafi daurin aure ne a ranar Juma’a 1 ga Mayu, a gidan abokinsa Zakari wanda za a yi ranar 2 ga Mayun nan. Matansa da ’ya’yansa sun jira shi amma bai koma gida ba. Da wayewar gari misalin karfe 8:00 sai muka samu labarin cewa Abdul Halidu dan marigayi Janar Halidu da ke zaune a Jaji, ya harbe shi kuma ya kai gawarsa ofishin ’yan sanda da ke Rigachikun.
A cewarsa, su ’yan uwan marigayin sun tafi ofishin ’yan sanda na Rigachikun inda aka tabbatar musu cewa gawar dan uwansu na ofishin amma wai ba za a ba su gawar ba tunda iyalansa sun ce za su kai kara kotu.
Da Aminiya ta tuntubi kakakin ’yan sandan jihar DSP Zubairu Abubakar ya ce rundunar ta kama wanda ake zargi da kisan hade da wasu mutum biyu.
“Suna ikirarin wai su ’yan sintiri ne suka je suka kashe mutum bisa zarginsa da satar shanu. Sun ce wai ya zo ne da nufin satar shanu amma babu shaidar cewa ya kora shanun. Saboda haka ne Kwamishinan ’Yan sanda ya ba da umarnin a mayar da lamarin sashin binciken manyan laifuffuka don ci gaba da bincike,” inji shi. DSP Zubairu ya ce dole sai an tabbatar da sanadin mutuwar marigayin kafin a bai wa ’yan uwansa gawarsa.