’Yan daba sun kashe ɗan sanda da duka har lahira a Adamawa

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce a gudanar da bincike tare da gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

’Yan daba sun kashe ɗan sanda da duka har lahira a Adamawa

‘Yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa, ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan wani ɗan sanda mai suna Ibrahim Maizabuwa.

Waɗanda ake zargin; Ezekiel Kefas, mai shekara 67 da Stephen Zabadi, mai shekara 44, dukkaninsu mazauna unguwar Wamsa Suwa a Ƙaramar Hukumar Lamurde.

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2024, bayan ɗan mamacin, Danlami Ibrahim Maizabuwa, ya kai wa ’yan sanda rahoto.

Bincike ya nuna cewa sun kashe ɗan sandan sannan suka birne shi a yankin bayan ya ziyarci abokinsa, Ezekiel Kefas.

A lokacin bincike, Ezekiel Kefas, ya bayyana cewa wasu matasa ne suka kashe ɗan sandan.

Ya ce ɗan sandan ya lalata kayayyaki a gidansa, har da tukunyar girki, sannan ya doki mutane.

Wannan ya sa mata da yara suka yi masa ihu, wanda hakan ya ja hankalin ’yan daba a yankin.

“Abokina ya fara ɓalle kayayyaki a gidana, sannan ya hau dukan mutane, wanda hakan ya sa mata da yara suka yi ihu.

“Sai wasu matasa suka zo suka yi masa dukan tsiya da sanduna wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

“Waɗanda suka kashe shi su ne Yakubu, Suleiman, da Kilyobas. Mun je gidajensu jiya amma ba mu same su ba,” in ji Ezekiel.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Morris Dankombo, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu.

Isra’ila ta tsagaita wuta a Lebanon

Za a yi sallar roƙon ruwa a Saudiyya

Kotun ta bai wa EFCC umarnin tsare Yahaya Bello

’Yan daba sun kashe ɗan sanda da duka har lahira a Adamawa