’Yan daba sun kashe mutum uku a Jihar Legas
Mutum uku sun rasu, wasu da dama sun ji munanan raununaka yayin da fada ya barke tsakanin ’yan garejin unguwar Gangare da na layin Lawani da ke cikin yankin Ijora Badiya da ke Jihar Legas.Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa mai suna Muhammad Baba Cakaraboti ya bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya auku […]

Mutum uku sun rasu, wasu da dama sun ji munanan raununaka yayin da fada ya barke tsakanin ’yan garejin unguwar Gangare da na layin Lawani da ke cikin yankin Ijora Badiya da ke Jihar Legas.
Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa mai suna Muhammad Baba Cakaraboti ya bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne da safiyar karshen makon da ya gabata.
Muhammad Baba ya ce, “Lamarin ya auku ne yayin da musu na ba-gaira-ba-dalili ya kaure a tsakanin wasu ’yan daba na layin Lawani da wani dan unguwar Gangare, sai kawai na ga daya daga cikinsu ya fasa kwalba ya caka wa daya, kafin wani lokaci sai jini ya rika zuba kamar ruwa, daga bisani da aka kai shi asibiti, sai kuma aka ce ya mutu”.
Ya cigaba da cewa, “Sai ’yan uwansa ’yan daba suka zo suna cewa sai sun dauki fansa. Washegari sai kawai suka dawo suna saran mutane, suna yankawa, suna kashe duk wanda suka samu. Suka rika fasa dakunan jama’a suna kwashe kayayyakinsu. Ni kaina ban tsira da komai ba, sai kayan da ke jikina, duk sun kwashe mini kayayyaki da kudi da kayan kallo”.
Ya bayyana cewa akwai wani makwabcinsa ma da aka fasa dakinsa aka kwashe masa kaya da kudi.
Ya kara da cewa mutane sun rika gudu domin tsira da rayukansu a lokacin da ’yan dabar suka zo daukar fansa. “Mata da maza kowa sai gudu yake yi, sai ka ce yaki. Na yi asara ta kai ta Naira dubu dari biyu da wani abokina mai suna Sama’ila shi ma an kwashe masa Naira dubu saba’in da wani mai suna Sarafa shi ma an dauke masa kayayyaki. Gaskiya sun yi barna sosai kuma sun sa jama’a sun yi asara da yawa”. Inji shi.
Ya bayyana cewa daga bisani ’yan sanda sun zo wurin tare da kama mutane da dama.
Saboda haka sai ya ce hankula sun kwanta komai ya koma daidai bayan hargitsin, amma Muhammed Baba ya ce shi ba zai koma wurin ba, saboda tsoron abin da ka iya biyo baya saboda alwashin da ’yan dabar suka yi na kone wuri gaba daya.
Rundunar ’yan sandan jihar ta bayyana cewa komai ya koma daidai bayan daukin da ’yan sanda suka kai wurin.