’Yan daba sun tarwatsa taron APC a Delta
’Yan daban sun ce tsohon yi awon gaba da shugaban matasan kan ki biyan su wasu kudade.
Gungun wasu ’yan daba sun tarwatsa taron Jam’iyyar APC tare yin awon gaba da tsohon Shugaban Matasan Jam’iyyar PDP, Kwamared Obaro Matthew Jagogo.
Yan daban sun tayar da hankalin jama’a ne a wurin taron da Kwamred Jagogo ya shirya da nufin sauya sheka zuwa APC a yankin Aladja na Jihar Delta.
- Batanci: Mun yaba da hukuncin rataye Abduljabbar —Majalisar Malamai
- An muttsuke mutane a wasan mawakin Najeriya a Landan
Sun zargi tsohon shugaban matasan na PDP da kin biyan su N400,000 da suke bin sa, amma suka shaida wa mahalarta taron cewa ba su da matsala da su.
Daga bisani suka yi waje da dan siyasar, suka casa makadin taron tare da lalata rumfunan da aka kayata wajen taron da su.
Kwamared Jagogo ya shirya taron ne da nufin bayyana barinsa PDP da kuma sauya shekarsa zuwa APC.
Manyan mutane kamar dan takarar Majalisar Tarayya Collins Egbetamah, Keston Okoro da Cid Williki na daga cikin wadanda ake sa ran zuwansu wajen taron kafin ’yan daban su tayar da yamutsin.
Shugaban Jam’iyyar APC na mazaba ta 10 a yankin Aladja, Mista Abeyi Lucky, wanda ya halarci taron don nuna goyon baya ga shugaban matasan, ya ce ba su yi tsammanin za a samu matsala a wajen ba.
“Ba mu yi tsammanin faruwar abu mai kama da haka ba.”
Ana fargabar za a iya samu hatsaniya tsakanin magoya bayan APC da ’yan jam’iyyar adawa a yankin.
Sai dai wasu manyan yankin sun yi kira da jami’an tsaro, Shugaban Karamar Hukumar Udu da sauran masu fada a ji da su sanya baki kan lamarin don tabbatar da doka da oda a yankin.