’Yan daba sun tayar da tarzoma a Legas
Hakan ta faru ne sa’o’i kadan kafin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a jihar, wanda Peter Obi na jam’iyyar LP ya yi nasara a kan dan asalin jihar, Bola Tinubu na Jam’iyyar APC.
’Yan daba dauke da makamai sun tayar da tarzoma tare da tarwatsa mutane a wasu kasuwanni a sassan Jihar Legas.
Hakan ta faru ne sa’o’i kadan kafin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a jihar, wanda Peter Obi na jam’iyyar LP ya yi nasara a kan dan asalin jihar, Bola Tinubu na Jam’iyyar APC.
Rahotanni daga Legas sun ce ’yan dabar sun kai wa ’yan kasuwa hari a Kasuwar Kayan Mota ta Ladipo, Kasuwar Balogun da ta Ebute-Ero.
Maharan sun kuma raunata mutane da dama tare da fasa shaguna suna yin awon gaba da kayan jama’a.
Hakan ta sa ’yan kasuwa suka rika cika bujensu da iska domin tsira da lafiyarsu
Abin da ya faru ya kuma haifar da zaman dar-dar da sauran kasuwanni irin Computer Village da ke Ikeja da Kasuwar Alaaba da dai sauransu da ke yankin Ojo.
Sai dai duk da haka kakakin ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya karyata rahoton rikicin.
A cewarsa, “’Yan kasuwar ne suka yi yarjejeniya cewa za su rufe kasuwa a ranar Lahadi da Litinin, ’yan dabar sun je ne su tabbatar da an cika alkawarin.“