’Yan daba sun yi wa dan sanda duka a Majalisar Jigawa

Wasu matasan da ake zaton ’yan dabar siyasa ne sun ba wani sajen din ’yan sanda da aka sakaya sunansa kashi a harabar Majalisar Dokoki ta Jihar Jigawa a daidai lokacin da Ma’aikatar Gona ta je kare kasafinta na bana a gaban majalisar.  dan sandan ya samu nasarar garkame matasan a ofishin ’yan sanda domin […]

’Yan daba sun yi wa dan sanda duka a Majalisar Jigawa
’Yan daba sun yi wa dan sanda duka a Majalisar Jigawa

Wasu matasan da ake zaton ’yan dabar siyasa ne sun ba wani sajen din ’yan sanda da aka sakaya sunansa kashi a harabar Majalisar Dokoki ta Jihar Jigawa a daidai lokacin da Ma’aikatar Gona ta je kare kasafinta na bana a gaban majalisar. 

dan sandan ya samu nasarar garkame matasan a ofishin ’yan sanda domin neman hakkinsa kan dukan da matasan suka yi masa.
Majiyarmu ta ce musabbabin fadan kudi ne wani dan majalisar ya ba ’yan dabar su raba amma sai wasu suka ce ba za a ba wa wasu ba suke neman cinyewa lamarin da ya sa fada ya kaure a tsakaninsu.
Majiyar ta ce ganin haka ne sajan ya yi musu tsawa kada su yi musu fada a harabar majalisar amma sai suka fusata suka auka wa sajen din da duka sai da aka kwace shi daga hannunsu.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa DSP Audu Jinjiri ya ce gaskiya ne an yi fada a harabar majalisar amma lamarin bai shafi dan sanda ba, babu wani dan sanda da aka yi wa duka fada ne a tsakanin ’yan jagaliyar siyasa.
Ya ce tuni ’yan sanda suka kama wadanda suka yi fadan su hudu har ma an gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Jihar don yi musu hukunci kan tuhumar laifin tayar da hankali da kokarin haifar da yamutsi a majalisa.
Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Alhaji Ibrahim Gwiwa ya ce an yi fadan ne a lokacin da babu kowa a majalisar kuma fadan ya faru ne a kan wasu ’yan kudi da wani dan majalisa ya wasu magoya bayansa.