’Yan dabar siyasa sun tarwatsa mutane a wurin zabe a Jigawa

Yan bangar siyasa sun tilasta mata da kananan yara tserewa zuwa gonaki domin tsira da rayukansu lokacin da aka gudanar da zaben cike gurbin dan majalisar jiha a karamar Hukumar Ringim da ke Jihar Jigawa.A lokacin zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, an samu hayaniya a kauyen Sankara da ke karamar […]

’Yan dabar siyasa sun tarwatsa mutane a wurin zabe a Jigawa
’Yan dabar siyasa sun tarwatsa mutane a wurin zabe a Jigawa

Yan bangar siyasa sun tilasta mata da kananan yara tserewa zuwa gonaki domin tsira da rayukansu lokacin da aka gudanar da zaben cike gurbin dan majalisar jiha a karamar Hukumar Ringim da ke Jihar Jigawa.
A lokacin zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, an samu hayaniya a kauyen Sankara da ke karamar Hukumar Ringim lamarin da ya sa mutane suka kaurace wa gidajensu
zuwa cikin gonaki domin tsira daga harin ’yan sara-suka da ake zargin Sanata danladi Sankara dan asalin garin ne ya kawo su daga Kano domin su tarwatsa zaben saboda ya cimma burinsa na siyasa.
Wani mazaunin Sankara, Malam Sani Adamu, ya zargi Sanata Sankara na Jam’iyyar PDP cewa yana kawo musu masifa a duk lokacin da za a gudanar da zabe a yankin “ko wannan zabe shi ne ya shigo mana da ’yan dabar siyasa suka aikata mana ta’addanci,” inji shi.
Ya ce suna tayar da hankali ne saboda sun fuskanci cewa ba za su kai labari ba, inda suka yi amfani da ’yan daba suka auka wa jami’an zabe da duka suka sace akwatin zaben lamarin da ya haifar da hayaniya aka sassari mutane da farfasa motoci ciki har da motar tsohon dan Majalisar Tarayya Alhaji Faruk Adamu Aliyu aka kuma ji wa biyu daga cikin na hannun damansa munanan raunuka da ya sa aka kwantar da su a asibiti.
Ya ce, ’yan sanda sun kama ’yan dabar ciki har da dan Sanata Sankara mai suna Auwalu danladi Sankara, amma ko kwana bai yi ba a hannun ’yan sandan wani babban dan siyasa ya je ya amshi belinsa.
Da yake jawabi Alhaji Faruk Adamu Aliyu ya ce abin da Sanata Sankara ya yi bai dace ba, “a ce wanda ya san doka shi ne zai rika yi wa doka hawan kawara, a ce ya dauko hayar ’yan dabar siyasa su auka wa mutanen garinsu ba su san hawa ba ballantana sauka,” inji shi.
Ya ce tun kafin zaben Sanata Sankara ya ce za su kashe mutane za su kone gidajensu za su yi
amfani da ’yan daba wajen yin ramuwa gayya.
Alhaji Faruk Aliyu ya soki jami’an tsaro kan sakacin da suka nuna domin sun sanar da su tun lokacin da ya yi ikirarin fatar baki cewar zai kawo ’yan dabar, kuma ga shi yana yawonsa babu abin da hukuma ta yi masa.
kokarin da wakilinmu ya yi domin jin tab akin Sanata Sankara kan wannan zargi ya ci tura, sai dai wani na hannun damansa ya ce, zargi ne marar tushe.