’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe
Rundunar ta ce za ta gurfanar da su a kotu da zarar ra kammala bincike.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar mutane a wajen cirar kuɗi a ATM.
Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem, ya ce an kama Umar Abubakar mai shekara 24 da Abdulaziz Mohammad mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano.
- PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027
- Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu
An kama su lokacin da suke ƙoƙarin yaudarar wani mutum a wajen ATM na bankin Fidelity da ke Damaturu.
Ana zargin matasan da amfani da wasu dabara wajen damfarar mutane ta hanyar nuna kamar suna taimaka musu, amma daga baya sai su sauya musu katin ATM.
A wani labari kuma, jami’an ’yan sanda a Potiskum sun kama Usman Suleman mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Babura, a Jihar Jigawa, bisa zargin satar Keke Napep.
An kama shi lokacin da mai mai babur ɗin ya je sallah a masallaci da ke kusa da bankin Access a garin Potiskum.
An kama shi a Jihar Bauchi yayin da yake ƙoƙarin kai Keke Napep ɗin zuwa Jihar Kano.
A halin yanzu, ana ci gaba da bincike kan waɗanda ake zargin kafin gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya jinjina wa jami’ansa bisa ƙwazon da suka nuna.
Ya kuma gargaɗi masu aikata laifi da su daina, inda ya tabbatar da cewa Jihar Yobe ba za ta zama mafaka ga masu aikata laifi ba.
Ya buƙaci al’umma da su ci gaba da kai rahoton duk wani abu da ya shige masu duhu zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.
Ya kuma gode wa al’umma bisa haɗin kai da taimako da suke bai wa rundunar.