’Yan dirama sun sha da kyar a garin Sabo-Abekuta

Wasu gugun matasan Hausawa mazauna unguwar Sabo Abeokuta sun yi dirar mikiya a wani gidan shirya wasan kwaikwayo da ke daura da unguwar, inda suka fatattaki ’yan wasan kwaikwayon, suka lalata masu ɗaukacin kayayyakinsu na maƙudan kudi.Matasan sun kai ga yanke wannan ɗanyan hukunci ne bayan da wasu baƙin ’yan wasan kwaikwayo daga garin Jos […]

’Yan dirama sun sha da kyar a garin Sabo-Abekuta
’Yan dirama sun sha da kyar a garin Sabo-Abekuta

Wasu gugun matasan Hausawa mazauna unguwar Sabo Abeokuta sun yi dirar mikiya a wani gidan shirya wasan kwaikwayo da ke daura da unguwar, inda suka fatattaki ’yan wasan kwaikwayon, suka lalata masu ɗaukacin kayayyakinsu na maƙudan kudi.
Matasan sun kai ga yanke wannan ɗanyan hukunci ne bayan da wasu baƙin ’yan wasan kwaikwayo daga garin Jos suka yada zango a unguwar, suka nemi izinin yin sana’arsu ta wasan kwaikwayon daga wajan sarkin Hausawan Abekuta, Alhaji Ibrahim Hassan, ya kuwa amince masu bayan da suka nuna masa takardun shaidarsu da na ƙungiyarsu.
Matasan sun nuna rashin yardarsu ga wasan kwaikwayon, domin a cewarsu shi baƙon abu ne a wajensu kuma hanya ce ta gurɓata tarbiyyar yaransu, don haka suka kai kukansu ga sarkin Hausawan domin dakatar da shirin.
A cewar Malam Ado, wanda ya shaida faruwar lamarin, matasan sun yi cincirundo a bakin fadar sarkin, suna dauke da sanduna, inda suka yi ta kururuwa suna cin alwashin ɗaukar doka a hannunsu matukar masarautar b ata yi wani abu ba.  “Ana cikin wannan hali ne sai wasu daga cikinsu suka fara dukan iska, suna bugun tankunan ruwa da ke harabar fadar. Daga nan sai sashin matasan suka nufi gidan shirya wasan kwaikwayon, suka rufe mutanen da duka mazansu da matansu, har sai da ta kai suna ƙoƙarin cire wa matan suturarsu. Ka ga waɗanda suke iƙirarin yin gyara fa ke nan.” Inji shi.
Ya ƙara da cewa matasan sun lalata dukkanin kayayyakin da ’yan wasan ke amfani da su, sun kuma yi musu munanan raunuka. “Kuma abin mamaki shi ne, babu wata tazara a tsakanin ofishin ’yan sanda da fadar sarkin Hausawan, da ma gidan diramar amma aka gaza sanar da hukuma ta kai wa waɗannnan baƙi ɗauki. Sai bayan da aka ci zarafinsu tsaf ne daga bisani jami’an ’yan sanda suka fasa taron matasan suka yi ta harba barkonon tsohuwa. A nan ne aka kwashe ’yan wasan kwaikwayon a mota aka ɓoye su a wani gida.
Ɗaya daga cikin ’yan wasan mai suna Muhammadu ya shaida wa Aminiya cewa baya ga munanan raunukan da matasan suka yi musu, sun lalata masu kayayykin aikinsu na kimanin Naira dubu 300 baya ga baburan hawa guda 2 da suka lalata. Ya ce sun yi mamakin abin da Hausawa ’yan uwansu suka yi musu domin wasan da suke yi bai saɓa ƙa’ida ba, baya ga haka sai da suka nemi izini kafin su fara. “Kullum tare muke Sallah da su, mu yi buɗa baki tare sai ga shi sun zo sun ci zarafinmu. A daren da suka far mana mun sami labarin irin mummunar manufarsu a kanmu, don haka ba mu yi ko wasan kwaikwayon ba amma duk da haka suka yi mana wannan aika-aika. Neman arziƙi muka fito ba tsiya ba, don haka ba mu da lokacin kai su ƙara, mun bar su da Allah, Shi ne zai saka mana.” Inji shi.
Ya ce a daren da matasan suka far musu, mutum ɗaya ne ya tsira da Naira dubu ɗaya a cikinsu. Da yawansu ko abin buɗe baki na azumi ba su samu ba, haka suka zarce da azumin, abin da ya sanya biyu daga cikinsu galabaita; Hakan ya sanya dole suka haƙura da azumin. “Mu a yanzu ba za mu iya ci gaba da zama a wannan gari ba amma babbar matsalarmu ita ce, ko kuɗin motar komawa gida ba mu da su, bayan kuwa an lalata mana kayayyakin da muke yin sana’ar mu da su.” Inji shi.
Wani mai yin sana’a a daura da wajan da rikicin ya faru, wanda ya so a sakaye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa rikicin ya so ya juye, ya koma na ƙaɓilanci. “Domin mai gidan diramar na da abokai Yarabawa waɗanda suke jin daɗin wasan kwaikwayon. Ganin yadda aka ci mutuncin ’yan wasan sai matasan Yarabawan suka ɗau sanduna da adduna yayin da a ɗaya ɓangaren su ma matasan Hausawan suka ɗauki nasu makaman. A haka aka fara artabu, ana doke-doke ana ta sumar da mutane. In ban da ɗaukin da jami’an ’yan sanda suka kai, da rikicin ya zama babba domin akwai baƙin da suka fara yin ƙaura suna barin unguwar, ganin an shafe yini 2 ana ba-ta-kashi.” Inji shi.
Babban jami’n ‘yan sanda mai kula da yankin da lamarin ya faru, DPO Mr. Jonathan Igwu, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya kuma shaida wa Aminiya cewa rundunarsu na ci gaba da yin bincike za kuma ta tuhumi matasan da ɓarnatar da dukiyar jama’a.
A nasa ɓangaren, mai hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Ogun DSP Muyiwa Adejobi ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ’yan sandan ta bayar da sammaci kuma za ta yi duk abin da ya dace domin hana ɗaiɗaikun mutane ɗaukar doka a hannunsu.