‘Yan fansho sun koka kan kin sanya su a cikin mafi karancin albashi
Masu karbar fansho a kananan hukumomin Jihar Sakkwato sun koka kan kin sanya su a tsarin biyan mafi karancin albashi a tsawon lokaci da gwamnatin Jihar ta yi. Sun bayyana cewa ba a yi musu adalci ba a bambanta su da takwarorinsu na jiha da tazara mai yawan gaske wajen biyansu hakkokinsu, ba su ci […]
Masu karbar fansho a kananan hukumomin Jihar Sakkwato sun koka kan kin sanya su a tsarin biyan mafi karancin albashi a tsawon lokaci da gwamnatin Jihar ta yi.
Sun bayyana cewa ba a yi musu adalci ba a bambanta su da takwarorinsu na jiha da tazara mai yawan gaske wajen biyansu hakkokinsu, ba su ci gajiyar karin da aka yi ba.
Tun ana biyan mafi karanci albashi 18,000 har ya koma 30,000, biyan fansho da ake yi masu bai sauya ba.
A wasu takardun koke guda biyu da shugabannin Hadaddiyar Hungiyar Fansho ta Ma’aikatan Kananan Hukumomi da Ma’aikatan Ilmi da na Lafiya suka aika wa Majalisar Dokokin jihar Sakkwato domin ta sanya baki ga wannan matsalar da suka yi ta bi hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Takardun dauke da sa hannun shugaba Ibrahim Asha Fura Muhammad da Sakatare Muhammad Garba, zuwa ga Shugaban Majalisar Dokokin Jihar a 27 ga Juli sun nemi ya shiga batun kan rashin biyan su hakkokinsu da ake yi wanda ya saba wa dokokin aikin gwamnati.
A bayanin sun ce ma’aikatan kananan hukumomi da ilmi da lafiya bayan sun kammala aikinsu a tsawon shekara 35, a tsarin sabon albashi na 18,000 da suke karba tsawon shekara uku, babu wannan tsarin na kari a fanshon Kananan Hukumomin Jihar Sakkwato.
“Duk tsarin albashi shi ne tsarin biyan fansho, takwarorinmu da ke aiki a matakin jiha an sanya masu wannan tsarin ana biyan su da mafi karancin albashi da aka amince da shi.
“Gaskiyar magana a misali wanda ya yi ritaya ma’aikaci ko malami a mataki na 14 karamin mataki na 4 Fanshonsa a wata dubu 32,923:52, garatitu kuma zai kasance miliyan 1,481,558:40.
Kamata ya yi fanshonsa ya zama dubu 54, 456:00, garatitu kuma miliyan 2,450,520.
Ma’aikacin lafiya shi ma da ya bar aiki a wannan matakin yana karbar 40,200:00 fanshonsa na wata, garatitunsa 1,700,000:00.
Amma in za a biya shi yadda ya dace fanshonsa zai zama dubu 220, 000:00 garatitu(CONHENSS) miliyan 9, 700,000:00.
Kan haka muke rokon ka ka taimaka mana a tabbatar da an rika biyan mu hakkinmu kamar yadda dokar aikin gwamnati ta tanadar ga wadan da suka yi ritaya”, a cewar bayanin.
Kungiyar ta sake tura takardar neman sanin matsayar da majalisa ta cimma kan kokensu a ranar 6 ga Junairu 2020, domin masu karbar fanso da al’ummar Jihar Sakkwato su san inda aka kwana sannan su san wace matsaya za su dauka a gaba.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin wadanda suka kai koken ya ci tura domin wani na kusa da su ya fada wa wakilinmu ba za su yi magana ba sai sun kai karshe da Majalisar Dokokin ta jiha, suna jira su ga matakin da za su dauka, kafin nan su gaya wa manema labarai matakin da za su dauka a gaba.