‘Yan fansho za su samu haƙƙoƙinsu bayan shekara 21 a Neja

Wasu sun yi ritaya shekaru 21 da suka gabata ba tare da an biya su haƙƙoƙinsu

‘Yan fansho za su samu haƙƙoƙinsu bayan shekara 21 a Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta fitar da Naira biliyan 25 domin biyan ma’aikatan da suka yi ritaya haƙƙoƙinsu na ƙarshe a faɗin jihar.

Gwamnan Jihar Neja Mohammed Umaru Bago ne ya bayyana cewa wasu ’yan fansho sun yi ritaya shekaru 21 da suka gabata ba tare da samun alawus-alawus ɗinsu ba, wanda hakan ya sa aka shafe shekaru da dama ana ta fama da ɓacin rai kafin gwamnatinsa ta shiga tsakani.

“Mun gama biyan waɗanda suka yi ritaya haƙƙoƙinsu. Wasu sun yi ritaya shekaru 21 da suka gabata ba tare da an biya su haƙƙoƙin fansho da wasu kudade ba.

“Wannan maƙudan kuɗaɗe na nuna jajircewar da gwamnatin ke yi wajen kyautata jin daɗin ma’aikatan jihar da suka yi ritaya.

“Idan ka ga yanayin wasu daga cikin waɗanda suka yi ritaya, za ka kusa zubar da hawaye.

“Idan aka la’akari da cewa bayan shafe shekaru 35 ana yi wa ƙasa hidima, sannan aka yi ritaya, amma maimakon a samu hutu, sai a fara sabon gwagwarmaya don samun haƙƙoƙi ku. yanzu wannan ya zama tarihi,” in ji Bago.

Ya ce, baya ga sauke nauyin waɗannan basussukan da aka daɗe ana jira, gwamnatin jihar ta kuma biya albashin N20,000 ga ma’aikatan gwamnati a karo na biyu cikin watanni biyu.

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa wannan wani muhimmin mataki ne na rage wa ‘yan fansho da suka yi ritaya, radadin da suke fuskanta.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS