’Yan fashi 24 sun shiga hannu a Legas
Kwamishinan ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.
An kama wasu mutum 24 da ake zargi da aikata fashi da makami da wasu laifuka a yankin Oshodi da ke Jihar Legas.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa, Tokunbo Wahab ne, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
- An kama ’yan talla da ke kai wa ’yan bindiga bayanai
- Mutum 6 sun jikkata, an ƙone kayayyaki a rikicin fili a Neja
Ya ce, “An kama wasu ‘yan fashi 24 a Oshodi jiya, kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya domin yanke musu hukunci.”
A gefe guda kuma Kwamishinan, ya bayyana cewa jami’an Sashen Kula da Magudanar Ruwa daga Ma’aikatar Muhalli da Ruwa ta Jihar Legas, sun fara rushe wasu gine-ginen da aka yi a kan magudanar ruwa a yankin Ajiran da ke ƙaramar hukumar Eti-Osa.
Kwamishinan ya ce matakin na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar, na dakile ambaliyar ruwa.
Ko a makon da ya gabata, sai da aka samu ambaliyar ruwa wadda ta yi sanadin lalacewar dukiyoyi masu tarin yawa, sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a jihar.