’Yan fashi 8 sun shiga hannu a Abuja
Rundunar ta kama masu laifin ne biyo bayan samun wasu bayanan sirri.
Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, ta kama wasu kasurguman ’yan fashi da makami guda takwas
Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Mista Benneth Igweh ne, ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da masu laifin a ranar Laraba.
- Gwamnati ta dauki ’yan sanda 50,000 aiki duk shekara — Shekarau
- Jami’ar Gombe ta ɗaga likafar malamai huɗu zuwa matsayin Farfesa
Ya ce wasu jami’an rundunar da ke yankin Mabushi ne, suka kama su a ranar Talata da misalin karfe 4 na yamma.
Ya ce an kama su ne biyo bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu kan yadda suke yi wa mutane fashi da makami.
A cewarsa rundunar ta bi su har maboyarsu, tare da sun damke su.
’Yan fashin sun bayyana cewar bindigogin da suke amfani wajen razana mutane na roba ne.
Kazalika, ya ce rundunar ta kama wasu mutum 79 da ake zargi aikata laifuka daban-daban a wani samame da suka kai yankunan Trademore, Galadimawa, Maitama da Gwagwalada.