’Yan fashi na ci gaba da barna a dazukan Birnin Gwari 1
’Yan fashi da makami dauke da manyan bindigogi na cin karensu babu babbaka a dazukan Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna da Faskari a Jihar Katsina da Tsafe a Jihar Zamfara da kuma Pandogari a Jihar Neja, inda suke hana mutanen yankunan sakat.Wakilinmu wanda ya ga fashi biyu a kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari […]

’Yan fashi da makami dauke da manyan bindigogi na cin karensu babu babbaka a dazukan Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna da Faskari a Jihar Katsina da Tsafe a Jihar Zamfara da kuma Pandogari a Jihar Neja, inda suke hana mutanen yankunan sakat.
Wakilinmu wanda ya ga fashi biyu a kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari a ranar Litinin da ta gabata, ya ce fashi na farko an yi ne a Kwanar-Mahaukaciya da karfe 7:00 na safe sannan aka yi na biyu kimanin kilomita biyar daga inda aka yi na farko da karfe 7:30 na safe.
Ya ce a fashin farko an tare titi ne da duwatsu na biyu aka tare manyan motoci a tsakiyar titi aka yi wa bayin Allah fashin kudi da wayoyin salula da sauran kayayykinsu.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa ’yan fashin sun yi zango a kauyen Jan-Birni ne da ke karamar Hukumar Birnin Gwari a gefen makarantar firamare inda suke cin karensu ba babbaka tunda hukuma ba ta kai musu farmaki ba.
Wakilinmu ya ce wata majiya ta shaida masa cewa kamar yadda Bafullatani ke rataya sanda ya shiga gari, haka ’yan fashin ke rataya bindiga su shiga gari domin karyawa ko sayo sigari ko su rika kwace da fashi kiri-da-muzu.
Wani mai unguwa a Birnin Gwari da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa yawancin ’yan fashin Fulani ne da ake zargi suna da ’yan rahoto a cikin jama’ar gari da kauyuka, inda ya roki gwamnati ta tallafa don samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Ya ce, “A cikin dardar muke in dare ya yi, sannan koda rana ma ba ma cikin kwanciyar hankali don haka ne Fulani masu kiwon shanu suke ta yin kaura zuwa Jihar Neja wanda haka ya janyo tsadar nono da nama da hatsi tunda mutane da yawa ba su samu damar yin noma ba, ko an yi musu fashin abin da suka noma.”
Binciken Aminiya ya gano cewa baya ga fashin shanu da kudi da sauran kayayyaki yanzu ’yan fashin sun fara fashin mata suna shiga da su daji ko su yi lalata da su a kan titi ana gani kiri-kiri. Kuma ta gano ’yan fashin na iya fitar dango kamar mutum 50 su zagaye wurin da za su yi wa fashi.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce idan sun sanar da sojojin da ke aikin tsaro kafin shiga garin Birnin Gwari, sai su ce ba a ba su izinin matsawa daga inda aka aje su ba.
Wani Bafillace da bai so a ambaci sunansa ya ce ya kamata gwamnati ta san cewa ana ta kashe bayin Allah da kuma satar mata a shige dajin da ke tsakanin jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da kuma Neja.
Jama’in gudanarwa na kungiyar Miyetti Allah ta kasa reshen Jihar Kaduna, Alhaji Husaini Salisu Kachia, Dallatun Ladugga, ya ce, “barayin zaune ne suka fi cutar da jama’a domin su suke kai rahoto su yi dillacin shanun da aka sato su yanka, su yi fawa su sayar. Kuma Fulanin ne aka fi yi wa fashin, su aka fi talautawa amma babu wani tallafi da ake ba su.”
Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Kaduna, Alhaji Shehu Ahmed (Giant) ya ce gwamnati na shirin samar da dauwamammen zaman lafiya a wannan yanki nan ba da bata lokaci ba.