’Yan fashi su yi wa matashi ruwan harsashi a Kalaba

Wani dan kasuwa mai suna Tijjani Bulama ya tsallake rijiya da baya, sakamakon ruwan harsashi da ake zaton ’yan fashi da makami suka yi masa a unguwar Ekorinim da ke Kalaba Jihar Kuros Riba. Yayin da suka yi wa gidansu dirar mikiya tsakar dare, inda suka yi wa daukacin mutanen gidan ruwan harsashi. Yanzu haka […]

’Yan fashi su yi wa matashi ruwan harsashi a Kalaba
’Yan fashi su yi wa matashi ruwan harsashi a Kalaba

Wani dan kasuwa mai suna Tijjani Bulama ya tsallake rijiya da baya, sakamakon ruwan harsashi da ake zaton ’yan fashi da makami suka yi masa a unguwar Ekorinim da ke Kalaba Jihar Kuros Riba. Yayin da suka yi wa gidansu dirar mikiya tsakar dare, inda suka yi wa daukacin mutanen gidan ruwan harsashi. Yanzu haka dan kasuwar na kwance a babban asibitin koyarwa na Jami’ar Kalaba,indayake karbar magani, a cewar Alhaji Umaru Hamman Joda, dan uwan majinyacin kamar yadda ya shaida wa Aminiya .

Ya ce, “da misalin karfe uku na dare ne wasu wadanda ake kyautata zato ’yan fashi da makami ne suka fada gidan ddan uwana mai suna Tijjani Bulama, domin su yi fashi,inda suka rika harbe-harbe cikin gidan har suka samu dan uwana a kirjinsa da kuma ciki. Allah dai yasa yana da sauran shan ruwa gaba, sai muka sanar wa ’yan sanda daganan gundumar gidajen ma’aikatan gwamnatin jiha wato “state housing”su kuma suka yi kokarin garzayawa da shi asibiti.
Alhaji Hamman Joda, yaci gaba da cewa “ a gidan sun yi fashin wata mota shi kuma dan uwana sun kwace masa wayoyinsa na hannu, tare da kudi da aka kiyasata za su kai Naira 500 suka tafi da su”.Babu hasarar rai sai dai ta dukiya,” inji shi.
Aminiya ta ziyarci asibitin, inda yake jinya, wanda kaddarar ta afka mawa dai likitoci sun ce yana bukatar hutu da kuma kulawa, don haka ba’a a samu jin ta bakinsa ba. Daga bisani mun tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kuros Riba, Hogan Bassey, wanda ya gaskata faruwar lamari ,sai dai ya ce suna gudanar da bincike.