’Yan fashi sun addabi mazauna Jalingo
Yan fashi da makami sun addabi mazauna garin Jalingo fadar gwamnatin Jihar Taraba a ’yan kwanakin nan inda suka kai farmaki a gidaje masu yawa suka yi awon gaba da kayyayaki na dubban nairori.Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa akalla a kowane dare barayi kan kai farmaki da manyan bindigogi a gidajen jama’a […]
Yan fashi da makami sun addabi mazauna garin Jalingo fadar gwamnatin Jihar Taraba a ’yan kwanakin nan inda suka kai farmaki a gidaje masu yawa suka yi awon gaba da kayyayaki na dubban nairori.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa akalla a kowane dare barayi kan kai farmaki da manyan bindigogi a gidajen jama’a masu yawa a sassa daban-daban na birnin.
Bincike ya nuna cewa ’yan fashin wadanda ke gudanar da mugun aikinsu na tafiya ne a ayarin mutum takwas zuwa goma dauke da miyagun makamai.
Wadanda aka yi wa fashin sun nuna damuwa kan rashin dauki da suke samu daga jami’an tsaro. Sa’an nan ’yan banga sun dakatar da ayyukansu saboda rashin samun tallafi daga gwamnati da kuma jama’a.
Aminiya ta gano cewa a mafi yawan lokuta ’yan fashin kan soma ayyukansu ne tun dare bai yi nisa ba, inda suke ce karensu ba babbaka.
Wani wanda ’yan fashin suka kai wa hari mai suna Malam Sadik Adamu ya ce ’yan fashin sun shiga gidansa ne dauke da bindigogi da wukake, yana cikin kallon labaran karfe 9:00 na dare a talabijin tare da iyalinsa.
Ya ce daya daga cikin ’yan fashin wanda yake zaton shi ne shugabansu ya umarci kowa ya kwanta kuma ya nuna masa bindiga ya umurce shi da ya kawo kudi maza-maza in ba haka ba zai kashe shi.
Malam Sadik ya ce ya kai shi dakinsa kuma yana kallo ’yan fashin suka bincike dukkan kayan da ke dakin da saura dakunan gidan don gano inda kudi suke. “Bayan sun karbe ’yan kudina da na iyalina sun kuma karbe wayoyina da na ’ya’yana da na matata da kwamfutoci da akwatunan talabijin na bango, sai suka umurce ni, in ba su mabudin motata, inda zuba kayan a ciki suka yi gaba,” inji shi.
Malam Sadik ya ce bayan ’yan fashin sun tafi ne ya nemi dauki daga makwabta inda aka sanar da ’yan sanda, kuma cikin daren ’yan sanda suka bi lungu-lungu don bin sawun bayarin amma ba su ji duriyarsu ba, sai dai daga baya an samu motarsa ’yan fashin sun yar da ita a gefen hanya kusa da babban tashar motar Jalingo.
A wani gidan mai a Jalingon ’yan fashin sun yi awon gaba da sama da Naira miliyan tara.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Taraba ASP Joseph Kwaji ya ce rundunar na iyakacin kokarinta don kare lafiyar al’umma kuma ya nemi mazauna Jalingo su rika kai rahoton duk wani ko wadanda ba su amince da take-takensu ba.