’Yan fashi sun addabi mutanen karamar Hukumar Agege

Ga alamu ’yan fashi da makami na cin karensu ba babbaka a unguwanni da dama da ke karamar Hukumar Agege a Jihar Legas.Binciken Aminiya ya nuna ’yan fashin, suna tafiya gungu-gungu ne suna shiga gidaje tare da kwace kudi da kadarori daga mutanen da ke zaune a gidajen.Unguwanni kamar Kwakwa Uku da Pen Cinema da […]

’Yan fashi sun addabi mutanen karamar Hukumar Agege
’Yan fashi sun addabi mutanen karamar Hukumar Agege

Ga alamu ’yan fashi da makami na cin karensu ba babbaka a unguwanni da dama da ke karamar Hukumar Agege a Jihar Legas.
Binciken Aminiya ya nuna ’yan fashin, suna tafiya gungu-gungu ne suna shiga gidaje tare da kwace kudi da kadarori daga mutanen da ke zaune a gidajen.
Unguwanni kamar Kwakwa Uku da Pen Cinema da Millero da titin Oniwaya da Markaz da Bagulori sun zama sansanin ’yan fashin inda suka mayar da su tamkar rijiyar yasa.
Wani mai suna Aliyu Tela ya bayyana cewa ’yan fashin sun shiga gidan wata mata mai abinci da ake kira Zuwaira, inda suka kwace mata kudi da gwalagwalai tare da sauran mutanen gidan, “Kuma  har suka gama abin da suke yi, babu dan sandan da ya zo wurin”. Inji shi.
Malam Abdullahi, wanda ’yan fashin suka shiga gidansu ya bayyana cewa Allah Ya taimake shi ba su yi masa rauni ba. “Ni ma sun shiga gidanmu, amma Allah Ya kiyaye ni ba su doke ni ba, sai dai sun shiga dakunan mutane da dama sun kwace musu kudi tare da wayoyin salula da sarka. Kuma sun shiga gidajen da ke kusa da mu kuma sun yi harbi da bindiga”. Inji shi.
Shi ma Malam Abubakar, mai sayar da kayan masarufi, ya tsegunta wa Aminiya ya ji cewa ’yan fashin sun shiga gidaje da dama kuma sun yi  barna sosai. Ya ce, “Sun shiga gidajen mutane unguwar Bagulori har sun kwace wa wata mata kudin cinikinta na abincin da take sayarwa”.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas Ngozi Braide ya ci tura, domin wayarta ba ta tafiya kuma ba ta ba da amsar sakon tes da aka tura mata kan lamarin ba.