’Yan fashi sun addabi unguwar Ijora-Badiya

Mazauna unguwar Ijora Badiya da ke Jihar Legas sun koka kan yadda ’yan fashi da makami ke kai musu farmaki babu kakkautawa. Wuraren da ’yan fashin suka kai wa farmaki sun hada da layin Relway da layin Oniyanrin da kuma layin Obanle. Mutanen yankin da dama da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana cewa […]

’Yan fashi sun addabi unguwar Ijora-Badiya
’Yan fashi sun addabi unguwar Ijora-Badiya

Mazauna unguwar Ijora Badiya da ke Jihar Legas sun koka kan yadda ’yan fashi da makami ke kai musu farmaki babu kakkautawa.

Wuraren da ’yan fashin suka kai wa farmaki sun hada da layin Relway da layin Oniyanrin da kuma layin Obanle. Mutanen yankin da dama da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana cewa harin da ’yan fashin suke kai musu ya jefa su cikin halin tsaka-mai-wuya.
Malam Yusufa Sani ya ce ’yan fashin sun sanya su kwana cikin fargaba da tashin hankali.
“Babu shakka muna cikin tashin hankali da fargaba. Kusan kullum sai ’yan fashi sun kawo mana hari. Wani lokaci su zo su yi ta harbe-harben kan mai-uwa-da-wabi, wani lokaci kuma sai kawai su rika shiga gidaje suna yi musu fashi ta hanyar kwace musu abin duniya. Akwai lokacin da suka zo suka shiga gidaje kusan 40 ba tare da ’yan sanda sun kawo musu dauki ba. Sai bayan sun gama cin karensu ba babbaka sannan sai ’yan sanda su zo suna kama mutane ba gaira ba dalili,” inji shi.
Shi kuwa Muhammad Usman ya bayyana cewa ’yan fashin sun shiga gidansu suka kwace musu kudade da wayoyin hannu.
“Ni ma sun shiga gidanmu a makon da ya gabata suka kwace mana kudi da wayoyin hannu. Da ma kofar gidanmu ba wata kofar kirki ba ce. Suna zuwa sai kawai suka karya kofar suka rika shiga daki-daki suna dukan jama’a suna kwace musu kudi da wayoyi,” inji shi.
Ita kuwa Madam Elisa Alayo ta bayyana cewa ’yan fashin sun ci zarafin mata da yawa a yankin.
“Mata da yawa sun gaya mani cewa ’yan fashin sun yi musu fyade bayan sun kwace musu kudi. Sannan kuma suka rika dukan su ba tare da jin tausayin su ba. Akwai gidan da suka shiga suka yi wa dukkanin ’yan matan gidan fyade. Haka suka rika yi ba tare da wata fargaba ba,” inji ta.
Jami’in ofishin ’yan sanda da ke yankin wanda ya ki bayyana sunannsa saboda wasu dalilai ya ce ba shi da hurumin yin magana da manema labarai. Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Kenneth Nwosu ya ci tura don bai amsa wayar da aka buga masa ba.