’Yan fashi sun halaka mutane a Kalaba

A kalla mutum uku aka kashe, wasu uku kuma suka samu munanan raunuka sanadiyar harbi a wani fashi da makami da aka yi a unguwar Esuk-utang da ke karamar Hukumar birnin Kalaba, Jihar Kuros riba .A wannan fashi da aka yi a unguwar, ya rutsa da wasu ’yan Arewa. uku suka rasa rayukan su, yayin […]

’Yan fashi sun halaka mutane a Kalaba
’Yan fashi sun halaka mutane a Kalaba

A kalla mutum uku aka kashe, wasu uku kuma suka samu munanan raunuka sanadiyar harbi a wani fashi da makami da aka yi a unguwar Esuk-utang da ke karamar Hukumar birnin Kalaba, Jihar Kuros riba .A wannan fashi da aka yi a unguwar, ya rutsa da wasu ’yan Arewa. uku suka rasa rayukan su, yayin da wasu mutum uku kuma ’yan fashin suka jikkata su, sanadin harbin bindiga.

Yusuf Sani, wanda aka fi sani da suna kaura da ’yan fashin suka harba a kafa, ya samu karaya a kafarsa ta dama, inda ya shaida wa wakilinmu cewa: “Mun gudu muka boye a daki suka yi kokarin shigowa suka kasa ji nake yi sun tafi, sai na ce mu bude kofa sun tafi, daga nan ne suka samu zarafin harbina. Shi kuma Malam Usman suka harbe shi suna dukan kansa har ya mutu.
“Ni kuma an cire min harsashi za su kai 50 irin na ’ya’yan boris,” inji shi.
Shi ma wani wanda ya kubuta a harin, Shehu Isah sakamakon harbi sa a kafa, har ya samu karaya yana jin jiki bai iya cewa uffan ba. Salisu A ci doya, wanda aka fi sani da suna baban Halima, shi ma a kafadarsa aka harbe shi, shi ne ma mutum na farko da ’yan fashin suka fara harbi. “Harsashi sama da 40 na ’ya’yan boris aka cire mini,”inji shi.
Dukiyar da barayin suka arce da ita an kiyasta cewa, za ta kai ta Naira milyan biyu, yayin da kadara kuma ta fi ta Naira milyan daya, ban da kudi da wayoyin salula na mutane da suka kwace.
Aminiya ta yi tattaki zuwa wurin da al’amarin ya faru, inda daya daga cikin shugabannin wurin mai suna Saidu Muhammad, wanda aka fi sani da suna, A boy, ya bayyana wa Aminiya yadda lamarin ya faru yace “ daren jiya alhamis ne da misalin karfe goma sha biyu na dare sai naji kira a wayata nace lafiya sai akace min ai barayi ne suka shigo anguwa wajen masallaci sonata harbe-harbe harma sun harbi mutane guda uku a wajen masallacin namu sannan kuma bayan sun gama fashin da suka tashi sai suka bar motar da suka zo da ita nan unguwar, suka kwace wata motar a wurin wani suka tafi.”injishi
A boy, ya ce da safe kuma muka ci gaba da kwasar wadanda suka ji raunuka aka kai su asibiti, gawarwakin wadanda aka kashe, aka yi jana’izar su. Mutane uku ne suka rasu, wadanda suka hada da Usman Gboko mai sana’ar wanki da guga da Barira Abdullahi, da Ilya Jos, wani bakanike ne.
Sai dai an wuce da gawar Usman Gboko zuwa garin su can Gboko don yi masa jana’iza,’’ in ji shi.
Da wakilinmu ya gama jin ta bakin shugaban wurin, sai Aminiya ta gana da wasu daga cikin wadanda fashin ya rutsa da su, da yake suna da sauran shan ruwa, suka bayyana yadda ’yan fasin suka dirar musu. Mika’ila Tela, ya ce: “To ni dai ina cikin shago ina dinkina sai na ji a na ta harbe-harbe, sai na dauka ko abin fashewa na wasan wuta ne da yara ke yi, wato ‘knock out.’ Na fito waje in ga ko mene ne, sai na ga an biyo ni da gudu, ana biyo ni da gudu, sai aka ce da ni in kawo wayata da kudi, wato barayi ke nan, don daya daga cikin ’yan fashin ma da ya ga ina kallon sa, sai ya ce me ya sa nake kallonsa, in ban daina ba zai harbe ni, sai na gudu na shiga cikin masallaci, suka biyo ni suna ta harbi a zo a same ni in ba da kudi da wayata, sai na ce musu ni ba ni da kudi, suka ya ga min wando, suka kwashe min kudi.
“ Allah ya taimake ni da kuma addu’o’in da na yi ta yi ne, Allah ya kwace ni a wurin su, da sun halaka ni ba,” a cewar Tela Mika’il.
Ya ce bai san adaddin ko Naira nawa ne suka kwace masa ba, da wayarsa ta hannu, domin kasuwanci yake yi, bai gama ba, balle ya kirga ya ga mai Allah ya ba shi, har wannan mai abkuwa ta afka musu.
Harin na da ’yan fashin suka kai wasu na danganta shi da siyasa, wasu kuWa na alakanta shi da sukurkucewar tsaro, domin wadanda aka zanta da su suka tofa albarkacin bakin su, sun shaida wa wannnaN jarida cewa, babu wasu jami’an tsaro da suka zo lokacin da ake yin fashin, har barayin suka ci karen su babu babbaka, suka tafi, sai daga bisani bayan wasu mintoci masu tsawo ne, sannan ’yan sandan suka zo wurin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan JiharKkuros riba, Hogan Bassey ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce rundunar su ba za ta yi kasa a gwiwa ba, sai sun zakulo barayin a duk inda suka boye, za su baza komar su.