’Yan fashi sun hallaka mutum 7 a harin Kasuwar Ngalda da ke Yobe
An kama jagoran ‘yan fashin, Datti Alhaji Dadji, wanda mazaunin garin Ngaldan ne.
Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun hallaka mutum bakwai yayin harin da suka kai shahararriyar kasuwar nan ta Ngalda da ke Ƙaramar Hukumar Fika a Jihar Yobe.
An ce ‘yan fashin sun arce da Naira miliyan 16.5 yayin harin da ya faru a ranar Litinin sa’ilin da mazauna yankin ke tashi daga kasuwar ta ngalda, wani kauye da ke kan iyaka da Jihar Gombe.
- Gwamnati ta musanta bai wa kamfanin bogi kwangilar titin Kano zuwa Abuja
- DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da afkuwar lamarin a sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Talata.
Ya ƙara da cewar an kama jagoran ‘yan fashin, Datti Alhaji Dadji, wanda mazaunin garin Ngaldan ne.
Yayin da yake janjata wa iyalan mutanen da harin ya rutsa da su, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmad Garba, ya ba da umarnin gaggawa na gudanar da bincike kan lamarin tare da yin kira da a kwantar da hankula.
Ya umarci jami’ansa su kama sauran mambobin gungun ‘yan fashin tare da yin kira ga jama’a da su taimaka wa rundunar da sahihan bayanai.