’Yan fashi sun hallaka mutum 9 a Birnin Gwari

Wasu ’yan fashi da makami da suka addabi jama’ar kauyukan karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kasuna sun sake kai hari a kauyan Gwaska da Gwauron Dutse inda suka hallaka mutum tara tare da raunata wasu.Wannan lamari ya yi matukar tayar da hankalin mazauna yankin inda rahotanni suka ce ’yan fashin sun fito ne daga […]

’Yan fashi sun hallaka mutum 9 a Birnin Gwari
’Yan fashi sun hallaka mutum 9 a Birnin Gwari

Wasu ’yan fashi da makami da suka addabi jama’ar kauyukan karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kasuna sun sake kai hari a kauyan Gwaska da Gwauron Dutse inda suka hallaka mutum tara tare da raunata wasu.
Wannan lamari ya yi matukar tayar da hankalin mazauna yankin inda rahotanni suka ce ’yan fashin sun fito ne daga dajin da ya hada yankin da Jihar Zamfara.
Bayanai sun ce ’yan fashin sun yi wa garin Gwaska dirar mikiya ne da misalin karfe 6:00 na safe suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.
Wani mazaunin yankin da ba ya son a ambaci sunansa, ya ce a cikin mutanen da ’yan fashin suka hallaka akwai mutum biyu da ke da matsalar tabin hankali.  “Da suka shiga Gwaska da misalin karfe 6:00 na safe sai muka rika jin harbe-harbe, suna bi suna kashe mutane. A garin Gwaska kawai sai da suka harbe mutum shida daga bisani suka wuce garin Gwauron Dutse inda suka harbe mutum uku suka raunata wasu,” inji shi.
Ya ce tuni an kwashe wasu da suka samu rauni zuwa asibitin garin Birnin Gwari domin yi musu magani.
Ya roki gwamnati ta kara tura musu jami’an tsaro domin a cewarsa a lokacin harin ’yan sintiri ne daga wani kauye suka kai musu taimako.
Shugaban karamar Hukumar Birnin Gwari Alhaji Musa Idris ya bayyana wa wakilinmu ta tarho cewa ’yan sintirin sun yi nasarar kashe biyu daga cikin ’yan fashin.
Ya ce ’yan sintirin sun yi kokari tare da hadin gwiwa da ’yan sanda aka samu nasarar korar ’yan fashin zuwa cikin dajin da suka fito.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya