’Yan fashi sun harbe ɗan sanda har lahira a Abuja
’Yan fashin da suka fito daga cikin wasu motoci marasa alama sun fara harbin ofishin ’yan sandan kafin su kutsa cikin bankin
Wasu ɓata-gari da ake kyautata zaton ’yan fashi da makami ne sun harbe wani sufeton ’yan sanda mai suna Abila har lahira a Abuja.
Wadannan ’yan fashi sun kai hari ne a reshen Bankin First Bank da ke Ƙaramar hukumar Abaji a yankin babban birnin tarayya Abuja.
Wani ɗan sanda mai suna Adamu ya ce, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:43 na yamma inda ’yan fashin da suka zo da yawa ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 suka fara kai farmaki ofishin ’yan sandan da ke kan hanyar Toto inda suka kashe sufeto Habila.
- Sallah: Hukumar sibil difens ta girke jami’ai 5,000 a Abuja
- An cafke mutum 6 da ke sayar wa masu garkuwa da mutane layin waya
Ya ce ’yan fashin da suka fito daga cikin wasu motoci guda biyu da ba su da alama sun fara harbin ofishin ’yan sandan, inda ya ce an harbe sufeton da ya mutu ne a ƙirji.
“Haƙiƙa Allah ne Ya tseratar da ni, domin a lokacin da waɗannan ɓata-garin suka sauko daga motar sai suka fara harbin ofishin ’yan sanda, yayin da na yi nasarar tserewa.
“Shi ma Sufeto ya riga ya tsere amma daga baya ya koma, a lokacin ne suka harbe shi a ƙirji,” in ji shi.
Wakilinmu ya kuma samu labarin cewa wasu tawagar ’yan fashin sun zarce zuwa bankin First Bank da ke shatale-talen unguwar, inda suka fara harbe-harbe a wurare daban-daban, yayin da ɗaya daga cikinsu ya lalata babbar ƙofar fita ta bankin ta hanyar buɗe mata wuta.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan bankin da ya zanta da wakilinmu da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ’yan fashin sun fara harbin wani jami’in tsaro ne a cikin banɗakin masu gadin bankin, kafin su shiga cikin bankin.
Ya ci gaba da cewa Kodayake ’yan fashin ba su samu nasarar shiga dakin da ake ajiye kuɗaɗe ba, amma duk da haka sun ƙwace kuɗaɗe a sashen hulɗa da jama’a na bankin.