’Yan fashi sun jikkata fataken shanu a Jihar Edo

A karshen makon da ya gabata ne ’yan fashi da makami suka tare wata motar ’yan kasuwa a kan hanyarsu ta zuwa fatauci, a ciki har da shugaban ’yan kasuwar na shanu reshen Jihar Edo, Alhaji Sani Musa Kwajole.Kamar yadda shugaban ya shaida wa Aminiya bayan da aka sallamo shi daga asibiti, ya ce: “Abin […]

’Yan fashi sun jikkata fataken shanu a Jihar Edo
’Yan fashi sun jikkata fataken shanu a Jihar Edo

A karshen makon da ya gabata ne ’yan fashi da makami suka tare wata motar ’yan kasuwa a kan hanyarsu ta zuwa fatauci, a ciki har da shugaban ’yan kasuwar na shanu reshen Jihar Edo, Alhaji Sani Musa Kwajole.
Kamar yadda shugaban ya shaida wa Aminiya bayan da aka sallamo shi daga asibiti, ya ce: “Abin da ya faru da mu shi ne, a ranar Asabar da ta gabata mun shirya tafiya zuwa kasuwar Chararanci ta Jihar Katsina, kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, sai motar da muka fara shiga daga Benin zuwa Arewa ta lalace a kan hanya, a kusa da Lokoja. Ganin haka sai muka samu wata motar muka tafi, har muka kai wani gari, inda muka tarar da barayi sun tare hanya.”
Ya ce al’amarin ya faru ne a cikin dare da misalin karfe 11:30. barayin suna dauke da miyagun makamai suka fada masu da duka kuma suka karbe abin hannunsu gaba daya har da wayoyin hannu. “Wani daga cikin barayin ya same ni da sanda, ya karya mani hannuna. Bayan da suka gama mana wannan cin mutunci sai suka juya a kan wata motar da ke biye da mu,” inji shi.
Ya ce cikin ikon Allah sai ’yan sandan da ke sintiri ne suka iso wurin, inda barayin suka fara musayar wuta da su, daga karshe da suka ga haza sai suka gudu cikin daji. Daga nan sai ’yan sandan suka kai su wani asibiti cikin garin Kaduna.