’Yan fashi sun kai farmaki gidan Sarkin Hausawan Jihar Kwara
Sarkin Hausawan Jihar Kwara Alhaji Abubakar Ibrahim ya tsallake rijiya da baya lokacin da wasu ’yan fashi da makami suka shiga gidansa da ke unguwar Zango a garin Ilori, suka rufe shi da duka, suka kwaci kudi masu yawa da wayoyin salula da wata karamar mota. Sai dai hakarsu bata cimma ruwa ba a dalilin […]

Sarkin Hausawan Jihar Kwara Alhaji Abubakar Ibrahim ya tsallake rijiya da baya lokacin da wasu ’yan fashi da makami suka shiga gidansa da ke unguwar Zango a garin Ilori, suka rufe shi da duka, suka kwaci kudi masu yawa da wayoyin salula da wata karamar mota. Sai dai hakarsu bata cimma ruwa ba a dalilin hanzarta sanar da ‘yan sanda irin halin da ake ciki wadanda suka garzaya da irin dabarunsu suka yi nasarar fatattakarsu tare da kwato motar sarkin da wata mota daban da barayin suka sato a wani wuri daban.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Kwara, DSP Fabode Olufemi ya tabbatar da aukuwar al’amarin. Ya ce, “Kodayake mun gano satattun motoci biyu da wasu manyan bindigogi, har yanzu ba mu kama kowa cikin barayin ba, bayan sun gudu sun bar ladarsu ne. Kuma mun gano babu wanda suka harba, sai dai sun jiggata sarkin da wasu mukarrabansa.”
Sarkin Hausawan ya shaida wa wakilinmu cewa yana gode wa Allah (SWT) da ya tserar da shi da iyalinsa da mutanen da suke tare a lokacin.
Zuwa lokacin rubuta wannan labari, mutane daga sassa daban-daban suna ta aikawa da sakon jaje ga sarkin, wanda aka nada watanni uku da wucewa.