’Yan fashi sun kashe dan banga sun raunata ’yan sanda uku a Bauchi

Wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kai hari ga gidan mai na A A Rano da ke Bauchi inda suka kashe dan banga daya tare da raunata ’yan sanda uku.Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi Mohammed Ladan wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya shaida wa manema labarai a shekaranjiya Laraba […]

’Yan fashi sun kashe dan banga sun raunata ’yan sanda uku a Bauchi
’Yan fashi sun kashe dan banga sun raunata ’yan sanda uku a Bauchi

Wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kai hari ga gidan mai na A A Rano da ke Bauchi inda suka kashe dan banga daya tare da raunata ’yan sanda uku.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi Mohammed Ladan wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya shaida wa manema labarai a shekaranjiya Laraba cewa, ’yan fashin su shida sun kai hari gidan man ne suka bindige dan bangar mai suna Umar Idris sannan suka yi fashin kudin da ba a ambaci yawansu bag a ma’aikatan gidan man.
Kwamishina Ladan ya ce, “Rahoto na iso mana muka mutanenmu da suka hada da jami’an yaki da fashi da makami da ‘’yan sanda daga ofishin yanki na Dutsen Tanshi zuwa inda wurin, sai dai lokacin da ‘’yan fashin suka hango mutanenmu, sai suka fara harbe-harbe, muka mayar musu da martani nan take, inda aka dauki minti 30 ana musayar wuta, ’yan bindigar sun ranta a na kare suka bi ta hanyar kauyen wasanni. Sun gudu sun bar bindigoginsu da motoci da sauran kayayyaki, kuma ’yan sanda uku sun samu kananan raunuka, biyu an harbe su a kafa daya a hannu kuma suna samun sauki.”
Kwimishinan ya kara da cewa, “Mun samu bindiga kirar AK 47 da makunshin harsashi uku da kuma harsasai 91 da wata karamar bindiga shake da harsashi da harsasanta takwas. Sai karamar bindiga da da mota kirar Toyota Starlet mai ruwan gwal mai Lamba YDB 217 AA sai Toyota Carina II mai Lamba AS 219 GME da wayar hannu da wau takardu masu muhimmanci.
Ya ce an fara bincike kan harin, kuma an killace yankin ana bincike don gano maharan wadanda suka gudu da raunin harsashi.
Ladan ya yi kira ga jama’a da kuma shugabanni da ma’aikatan asibitocin da ke jihar su taimaka wa ’yan sanda da bayanan duk wani mai jinya da suka gani da raunin harbin bindiga.
Wata majiyar jami’an tsaro ta ce motocin da maharan suka gudu suka bari sun yi kaca-kaca da jini.