’Yan fashi sun kashe mutum 3 yayin fashi a banki
Sun kwace kudi masu yawa a hannun wani mutum a banki.
Mutum uku da suka hada da dan jarida, dan sanda da dan acaba sun mutu bayan ’yan fashi sun bude musu wuta a wani banki a yankin Ilara-Mokin na Karamar Hukumar Ifedore a Jihar Ondo.
Dan jaridar mai suna Olubunmi Afuye, ya gamu da ajalin nasa ne bayan halartar taro a Jami’ar Fasaha ta Akure, wadda kuma shi ne sabon kakakinta.
- ’Yan bindiga sun kashe Janar din soja, sun sace matarsa
- Gwamnati ta ayyana hutun Babbar Sallah a Najeriya
’Yan fashin sun biyo wani mutum ne da ya dauko kudi zuwa banki, inda isarsu a bankin ke da wuya suka harbe wani jami’in dan sanda.
Bayan da ’yan fashin suka karbe kudin daga hannun mutumin da suka biyo, sai suka harbe wani dan acaba a lokacin da suke kokarin tserewa.
’Yan fashin sun harbe dan jaridar ne a kan titin Ilara zuwa Akure, a yayin da suka lura yana kokarin tare musu hanya.
Wata majiya ta ce barayin sun tsere ta hanyar Ikota inda suka rika harbi a iska don firgita mutane.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ondo, Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da faruwar fashin da kuma mutuwar dan sanda da dan acabar.