’Yan fashi sun kashe mutum hudu a Birnin Gwari

A ranar Asabar din da gabata ce wasu ’yan fashi da makami suka far wa wasu kauyuka a karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna inda suka halaka mutum hudu tare da ji wa wasu biyu rauni.kauyukan da ’yan fashin suka kai wa hari su ne Gwaran Dutse da Gwaska da Unguwar Ridi da […]

’Yan fashi sun kashe mutum hudu a Birnin Gwari
’Yan fashi sun kashe mutum hudu a Birnin Gwari

A ranar Asabar din da gabata ce wasu ’yan fashi da makami suka far wa wasu kauyuka a karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna inda suka halaka mutum hudu tare da ji wa wasu biyu rauni.
kauyukan da ’yan fashin suka kai wa hari su ne Gwaran Dutse da Gwaska da Unguwar Ridi da wasu unguwanni da ke kewaye da kauyukan. Wannan al’amari ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yamma lokacin da akasarin mutanen garin suke gida suna hutawa.
Majiyarmu ta ce da zuwan ’yan fashin sai suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare da harbin duk wanda suka gani a waje ko a kan hanya, al’amarin da ya tada hankalin mutanen kauyukan wadanda suka rika fitowa daga cikin gidajensu suna gudu domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin kauyen da bai so a ambaci sunansa ba ya ce suna gida a lokacin da ’yan fashin suka diro kauyen. “Muna cikin gida sai kawai muka fara jin karar harbin bindiga. Gaskiya manyan bindigogi suka zo da su, daga nan sai muka fito mazanmu da matanmu da yara muka bar gidajenmu. Wadannan ’yan fashi sun dade suna addabarmu, kuma babu ’yan sanda ko wasu jami”an tsaro a garin da za su tunkari ’yan fashin. Wannan ya sa duk muka gudu domin tsira da rayukanmu. Muna neman gwamnati ta kawo mana dauki domin muna cikin tsoro da tashin hankali,” inji shi.
Bayanai sun ce ’yan fashin sun je ramuwar gayya ce kan artabu da suka yi da ’yan sintirin garin a ranar Larabar makon jiya. An ce a wancan lokacin ’yan sintirin sun yi nasarar yi wa wasu daga cikin ’yan fashin raunuka, kuma hakan ya sa ’yan fashin suka sake dawowa domin ramuwar gayya.
Yanzu haka akasarin mutanen kauyukan da suka bar gidajensu sun fake ne a makarantar firamare da ke Doka wasu kuma na kwance a asibitin Doka domin karbar magani.
A wata sabuwa, Hukumar Bada Tallafi t a kasa (NEMA) ta raba wa ’yan gudun hijirar kauyukan da harin ya shafa wadanda ta ce sun kai dubu uku abinci da magunguna. Hukumar ta kuma tabbatar cewa akalla mutum hudu ne suka rasu sannan biyu suka samu raunuka.
Gwamnan Jihar Alhaji Ramalan Yero ya yi Allah wadai da harin inda ya ce gwamnatinsa za ta yi kokarinta wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar yankin da jihar baki daya.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Olufemi Adanaike ya ce bai samu labarin abin da ke faruwa a garin ba har zuwa lokacin da aka tuntube shi.