’Yan fashi sun kwace motar Gwamnan Jigawa
Wasu da ake zaton ’yan fashi ne sun kwace mota kirar Toyota landkurusa mallakar gidan Gwamnatin Jihar Jigawa a ranar Litinin da ta gabata, kuma motar na cikin jerin motocin Gwamnan Sule Lamido. Direban da aka kwace motar a hannunsa, yana tafiya ne da misalin karfe tara na dare, yayin da barayin suka tare shi […]
Wasu da ake zaton ’yan fashi ne sun kwace mota kirar Toyota landkurusa mallakar gidan Gwamnatin Jihar Jigawa a ranar Litinin da ta gabata, kuma motar na cikin jerin motocin Gwamnan Sule Lamido.
Direban da aka kwace motar a hannunsa, yana tafiya ne da misalin karfe tara na dare, yayin da barayin suka tare shi da bakin bindiga a daidai shatale-talen bypass da ke Dutse Don haka gidan gwamnatin ya sanar da rundunar ’yan sandan jihar halin da ake ciki, tuni ’yan sanda suka tsare direban don ya amsa tambayoyin da suka shafi harkokin tsaro, ta yadda za a samu cikakken bayani.
Da yake tabbatar da labarin, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa, Mataimakin Sufuritandan ’yan sanda, DSP Abdu Jinjiri, ya ce gaskiya ne an samu batan mota a wajen direban gidan gwamnati, mai suna Auwalu Umar, wanda ke tsare a hannun jami’ansa don amsa wadansu tambayoyi, inda ya ce motar Toyota ce kirar landcruiser, amma dai bai fadi lambar motar ba.
Bincike ya tabbatar da cewa motocin ana sanya musu na’urar tsaro ta yadda babu wanda ya isa ya sace su, amma wani abin mamaki sai ga shi an ce an samu ikon sace daya daga cikin motocin, wadda ke cikin jerin motocin hawan gwamna.
Ya ce har yanzu babu labarin motar, domin ’yan sanda sun dukufa wajen gano inda aka yi da motar gidan gwamnatin.