’Yan fashi sun kwace motar Kakakin Gwamnan Jigawa
Kwanaki biyu da nada tsohon Editan jaridar Aminya mukamin Kakakin Gwamnan Jihar Jigawa Malam Bello Muhammad Zaki, ’yan fashi da mukami sun tare shi a kan hanyar Kano zuwa Kazaure inda suka kwace motarsa. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:55 na yamma a ranar Lahadin da ta gabata.’Yan fashin sun tsare Malam Bello […]
Kwanaki biyu da nada tsohon Editan jaridar Aminya mukamin Kakakin Gwamnan Jihar Jigawa Malam Bello Muhammad Zaki, ’yan fashi da mukami sun tare shi a kan hanyar Kano zuwa Kazaure inda suka kwace motarsa.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:55 na yamma a ranar Lahadin da ta gabata.
’Yan fashin sun tsare Malam Bello Zaki ne tare da ’yarsa da abokansa a kan hanyarsu ta komawa gida, bayan shi da abokan tafiyarsa sun dauka ’yan sanda ne saboda suna sanye da kakin ’yan sanda a daidai wani gandun daji da ke karamar Hukumar Makoda da ke Jihar Kano.
Majiyarmu ta ce ’yan fashin sun tsare mutane da dama inda suka kwace masu kudi da kadarori, sannan suka zabi motoci biyar suka yi awon gaba da su.
Motar Kakakin Gwamnan mai suna Scongwong Korondo mai launin toka tana da lamba APP 337 KJ kuma bayan kwace ta sun juyo zuwa Kano ne maimakon hanyar dambatta, inda a kokarin gudu daya daga cikin motocin da suka kwace ta yi hadari.
Alhaji Bello Zaki ya shaida wa ’yan sanda a karamar Hukumar Makoda lokacin da yake gabatar da korafinsa cewa wadanda suka tare su suna dauke da makamai masu hadari, ya ce bayan daya daga cikin motocin da suka kwace ta samu hadari ne ’yan fashin suka gudu daji, inda aka samu katinsa na cire kudi a banki (ATM) da wayar ’yarsa da katin shaidar aikinsa a cikin motar.