’Yan fashi sun manta wayarsu a gidan mai
Sun daure masu gadin gidan man a cikin bandaki yayin da suke aikata fashin.
Wasu ’yan fashi sun manta da wayar salularsu a wani gidan mai da suka yi wa fashi da tsakar dare a garin Jalingo na Jihar Taraba.
Aminiya ta gano cewa a ’yan fashin sun kutsa gidan man Muhaunshant da ke kan hanyar garin ne da talatainin daren ranar Talata, suka daure masu gadi, suka kulle su a bandaki.
- El-Rufai ya sallami masu rike da mukaman siyasa 19
- Europa: An kai wa magoya bayan Man U hari a Poland
A yayin aika-aikan, ’yan fashin sun kashe wutar gidan man don samun sukunin yin barnar ba tare da an hango su ba a cikin duhun dare.
Miyagun sun kuma yi awon gaba da daukacin cinikin man da aka yi a ranar da kuma wasu muhimman abubuwa masu tarin yawa.
Sai dai kuma a garin tafiya daya daga cikinsu ya manta wayarsa, wadda jami’an ’yan sanda suka gano a lokacin da suke bincike bayan faruwar lamarin.
Mai gidan man, Alhaji Umar Yola ya tabbatar da labarin fashin tare da samun wayar ’yan fashin a cikin gidan man.
Shi ma kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da samun wayar a gidan man bayan zuwan ’yan sanda domin gudanar da bincike.