’Yan fashi sun sace jarirai uku a asibitin Kalaba
Wadansu mutane da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun yi wa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba dirar mikiya a ranar Lahadin da ta gabata, inda bayan fashin suka yi awon gaba da jarirai uku. Wakilinmu ya samu labarin cewa cikin dare ranar Lahadi ne ’yan fashin sun yi wa dakin da matan masu […]
Wadansu mutane da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun yi wa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba dirar mikiya a ranar Lahadin da ta gabata, inda bayan fashin suka yi awon gaba da jarirai uku.
Wakilinmu ya samu labarin cewa cikin dare ranar Lahadi ne ’yan fashin sun yi wa dakin da matan masu haihuwa kawanya, suka dira musu suka bubbugi wadansu matan sannan suka kwace wayoyin ma’aikata da na majinyata bayan sun umarci kowa ya kwanta rub-da-ciki ya rufe idonsa.
Aminiya ta ziyarci asibitin a ranar Talata domin jin yadda lamarin ya faru, kuma wadanda wakilinmu ya zanta da su da suka bukaci a sakaye sunansu sun ce barayin da dauke da miyagun makamai sun shigo musu kuma babu wani da ya rufe fuskarsa, suka ce kowa ya kwanta suka kwace wayoyin hannu da kudade da kuma daukar jarirai uku suka tafi da su.
Wata mata da ba a sace jaririnta ba, mai suna Helen Ekeng ta shaida wa wakilinmu cikin firgici cewa sun ga tashin hankali, “Barayin sun ce mana kowa ya kwanta kasa ya yi rub-da-ciki ya rufe idonsa,” inji ta.
Haka kuma wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa wannan ne karo na biyu da irin hakan ke faruwa a asibitin, inda ta yi zargin akwai sakaci wajen daukar matakan tsaro a asibitin kwarai da gaske.
Da Aminiya ta tuntubi Daraktan Asibitin, Farfesa Thomas Agan game da lamarin, sai ya ce, “Ku dai idan ban da tsegumi babu abin da kuka fi mayar da hankali a kai, me ya hana ku zuwa taron da muka yi na kwararrun likitoci kwanakin baya?”
Daga bisani daga ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce babu abin da za su iya yi kan lamarin, sai dai su yi fatan Allah Ya bayyana jariran da aka sace.
Jami’in ’yan sanda mai kula da sashen aikata miyagun laifuffuka na hukumar a Jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, inda ya bayyana cewa, suna jiran a sanar da su game da faruwar lamarin, idan har hakan ya faru, domin har yanzu labarin bai iso gare su ba.