’Yan fashi sun sace rigar amarya ana shirin biki

Duk da mun sanar da ’yan sanda, na fidda rai rigar ba za ta dawo ba.

’Yan fashi sun sace rigar amarya ana shirin biki

’Yan fashi sun bar wata amarya cikin zullumi bayan sun sace rigar bikinta a wurin cinkoson ababen hawa.

A wani sako da ta wallafa a dandalin sada zumunta, amaryar mai suna Jennine Naidoo, ta ce lamarin ya faru ne bayan cinkoson ababen hawa ya rutsa da su suna tsakar tafiya a cikin mota tare da mahaifinta.

Naidoo ta yi bayanin cewa a wannan makon ne aka sace rigar bikin yayin da suke kan hanyar zuwa kaiwa wani tela gyaranta a yankim Durban CBN na Kasar Afirka ta Kudu.

Naidoo wadda a ranar Asabar ta mako mai zuwa za ta shiga daga ciki, ta ce da dade tana ajiyar rigar a shirye-shiryen da take yi na bikinta.

Ta ce ba su yi aune ba ne aka sace rigar wadda ke bayan motar sakamakon cinkoson ababen hawa da suka riska a dalilin gobarar wani katafaren shago da ke kan hanya.

Naiddo wadda ta ce tuni sun shigar da korafi kan lamarin zuwa ga ’yan sanda, sai dai ta ce duk da haka ta fidda rai rigar ba za ta dawo ba.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Tags