’Yan fashi sun shiga tarkon ’yan banga a Benin

Wani shiri  da shugabannin ’yan Arewa mazauna Zangon Eyaen suka fara gudanarwa na tankade da rairaya da nufin kakkabewa tare da kawo karshen boyon miyagu masu aikata fashi da makami da ake zargin suna da mabuya a wurare daban-daban a zagayen babbar kasuwar shanu ta Benin, ya soma aiki.A wani yunkuri da ’yan banga suka […]

’Yan fashi sun shiga tarkon ’yan banga a Benin

Wasu daga cikin wadanda aka kama ana zarginsuWani shiri  da shugabannin ’yan Arewa mazauna Zangon Eyaen suka fara gudanarwa na tankade da rairaya da nufin kakkabewa tare da kawo karshen boyon miyagu masu aikata fashi da makami da ake zargin suna da mabuya a wurare daban-daban a zagayen babbar kasuwar shanu ta Benin, ya soma aiki.
A wani yunkuri da ’yan banga suka yi na baya-bayan nan, sun kama wasu mutum bakwai, wadanda har da mata a cikinsu da ake zargin ’yan fashi ne.
Shugaban ’yan bangan kuma Sarkin gainakai na Benin, Alhaji Shu’aibu Muhammed ya bayyana wa Aminiya haka kuma ya ce, “Wannan kamun da muka fara yi somin-tabi ne, domin za mu ci gaba da shi har sai mun tabbatar komai yana tafiya daidai a wannan zangon da ma kasuwar baki daya. Na sani da dama, wadanda ba su fahince mu ba, za su dauka kamar muna musguna wa ’yan uwa ne, amma ya kamata su gane ba ma nuna wani bambabci a cikin kama wadannan miyagun iri”.
Shugaban ya ce wadanda suka hannunsu sun hada da Muhammed Bello da Shehu Ali da Abubakar Ibrahim da Bello Muhammed da kuma wasu mata su biyu, wato Balki ’yar Bagobira da Binta Ayuba, wadada dukansu za su kasance manuniya ga sauran, wadanda ya bukaci su shafa wa kansu ruwa su komo daga rakiyar miyagun dabi’u.
Alhaji Shu’aibu ya koka kan rashin kayan aiki da za su tinkari miyagun, don haka ya roki gwamnatin Jihar Edo ta taimaka ta sama musu kayan aiki irin na zamani. “kungiyarmu tana bukatar taimako daga  gwamnatin jiha na kayan aiki domin tinkarar duk  wani kalu-bale na masu aikata miyagun ayyuka”, inji shi.