’Yan fashi sun yi awon gaba da miliyoyin Naira a kantin Masha- Allahu

Wasu ’yan fashi biyu a kan babur a rukunin kantin Masha-Allahu da ke garin Bunza a Jihar Kebbi sun yi awon gaba da miliyoyin Naira.A lokacin da wakilinmu ya isa garin Bunza, ya gana da Alhaji Abubakar Aliyu Bunza mai wannan makeken kanti kuma yana cikin kantin a lokacin da ’yan fashin suka je kantin […]

’Yan fashi sun yi awon gaba da miliyoyin Naira a kantin Masha- Allahu
’Yan fashi sun yi awon gaba da miliyoyin Naira a kantin Masha- Allahu

Wasu ’yan fashi biyu a kan babur a rukunin kantin Masha-Allahu da ke garin Bunza a Jihar Kebbi sun yi awon gaba da miliyoyin Naira.
A lokacin da wakilinmu ya isa garin Bunza, ya gana da Alhaji Abubakar Aliyu Bunza mai wannan makeken kanti kuma yana cikin kantin a lokacin da ’yan fashin suka je kantin ya shaida wa Aminiya cewa bayan sun gama Sallar Isha’i suna cikin shago su uku, mutum biyu suna sayen kaya, yana daga kansa sai ya ga wani mutum dauke da buhu. Ya ce shigowarsa ke da wuya sai ya bude buhun ya zaro bindiga ya umarce su kowa ya kwanta kasa ko ya harbe su.
Alhaji Abubakar Aliyu ya ce bayan sun kwanta a kasa sai ya tambaye su wane ne mai shagon, sai ya ce ga shi sai dan fashin ya ce masa ya kawo kudi. “Nan da nan na nuna masa inda kudin suke, ya sa hannun ya kwashe ya zuba cikin buhun, bayan ya gama kwashe kudin sai ya tambaye ni ina sauran cinikin da na yi jiya da shekaranjiya, na ce masa na sawo kaya, ya ce ina katin waya da nake sayarwa na ce masa na bar sayarwa,” inji shi.
Ya ce dan fashin ya gama abin da yake yi a cikin kantin sai ya ce masa ya kwanta a kasa, daya dan fashin yana tsaye bakin shagon rike da bindiga duk ya kori jama’ar da ke bakin titi ta harba bindiga da ya yi ta yi ba kakkautawa.
Shugaban ’Yan sandan Bunza (DPO) ya tabbatar da aukuwai lamarin, ya ce ba zai ce komai ba, suna bincike sai sun gama.