’Yan fashi sun yi hatsari a hanyarsu ta tserewa
’Yan fashin sanye da kayan ’yan sanda sun yi hatsari a hanyarsu ta kai motar Legas.
Wasu ’yan fashi sanye da kayan ’yan sanda sun yi hatsari a motar da suka yi fashinta, a garin tserewa da ita.
Bayan kwace motar, kirar Toyota Camry, a hannun mai ita da karfin bindiga, ’yan fashin sun shafe daruruwan kilomitoci domin tserewa da ita su kai ta Legas, amma suka yi mummunan hatsari.
- Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi Sheikh Gumi a kan tozarci
- Maganin gargajiya ya yi ajalin mutum 10 ’yan gida daya
“Mai motar da ya taso takanas daga Jihar Ondo ya ce mutum biyar ne sanye da kayan ’yan sanda suka kwace ta a hannunsa da karfin bindiga, suka yi wurgi da shi, sannan suka tafi da ita,” inji Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, inda motar ta yi hatsari da ’yan fashin.
Kakakin Rundunar, Abimbola Oyeyemi ya ce motar satar ta yi hatsari da uku daga cikin ’yan fashin da ke cikinta ne a garin Ode Remo na Karamar Hukumar Remo ta Arewa a Jihar ta Ogun.
Ya ce daya daga cikin ’yan fashin ya mutu, ragowar biyun kuma sun samu munanan raunuka, amma an garzaya da su zuwa asibiti, inda ’yan sanda ke tsare da su.
Oyeyemi, ya ce DPO na Ode Remo, ya tabbatar da samun rahoton cewa motar da ta yi hatsarin an yi fashinta ne.
Ya ce an Kwamishinan ’yan sandan Jihar ya sa a mayar da ’yan fashin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin kammala tattara bayanai, a gurfanar da su a kotu.