’Yan fashi sun yi wa Ali Nuhu kakat
A ranar Juma’ar da ta gabata ne ’yan fashi suka tare jarumi Ali Nuhu a kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kano don halartar bikin karrama ’yan fim da kamfanin sadarwa na MTN ya shirya. Sun tare jarumin ne da misalin karfe 8 na dare bayan ya bar Zariya kafin ya karasa Kaduna.Jarumin ya bayyana […]
A ranar Juma’ar da ta gabata ne ’yan fashi suka tare jarumi Ali Nuhu a kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kano don halartar bikin karrama ’yan fim da kamfanin sadarwa na MTN ya shirya.
Sun tare jarumin ne da misalin karfe 8 na dare bayan ya bar Zariya kafin ya karasa Kaduna.
Jarumin ya bayyana ’yan fashin sun kwace masa sabuwar motarsa kirar Anaconda ruwan toka da wayoyinsa kirar Samsung d5 guda uku da laptop da kayan sawa fiye da kala 20, sai dai ya ce ba su taba lafiyarsa ba.
Jarumin ya bayyana al’amarin da ya faru da shi mukaddari daga Ubangiji.
“Wannan abu da ya faru da ni mukaddari daga Allah (SWT), Yana jarraba bawanSa ta kowane hali. Ranaku na duniya iri biyu ne; ranar farin ciki da kuma ta bakin ciki, idan kana cikin ranar farin ciki, to kada ka yi dagawa, idan kuma kana cikin ta bakin ciki to ka kasance mai juriya da hakuri. Yana daya daga cikin imani ka yi imani da kaddara mai kyawu da marar kyawu. Allah ne Ya ba ni wadannan kayayyakin da aka kwace kuma Shi ne zai mayar mini da ninkinsa.” Inji Ali Nuhu.
Ya bukaci masoyansa da su ci gaba da addu’a domin ita ce takobin mumuni, kuma ba ta faduwa kasa banza.
Duk da abin da ya faru jarumin ya halarci bikin karrama ’yan fim da aka yi a Abuja, inda ya lashe kyautar Gwarzon Jarumi mafi fice, inda masoya suka zabe shi ta hanyar aika sakonni zuwa wata lamba da kamfanin sadarwa na MTN ya bayar.